Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta kasa (ICPC) ta tabbatar da kama Mista Oladipo Daniel Oyebanjo, wanda aka fi sani da D’Banj.
A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar ICPC, Misis Azuka Ogugua ta fitar, ta ce ana zargin D’Banj ne da laifin karkatar da kudaden shirin N-Power.
Shirin N-Power wani shiri ne da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa a ranar 8 ga watan Yuni, 2016, domin magance matsalolin rashin aikin yi da karfafawa matasa gwiwa, da kuma taimakawa wajen bunkasa zamantakewa.
“A bisa hakkin da ke kanmu, Hukumar ICPC ta samu koke-koke da dama kan karkatar da kudaden N-Power da suka kai biliyoyin Naira biyo bayan amincewa da fitar da kudaden ga wadanda suke cin gajiyar shirin. Yawancin masu cin gajiyar shirin N-Power sun koka kan rashin biyansu kudaden su na duk wata bayan kuma gwamnatin tuni ta fitar da kudaden.” inji wani bangare na sanarwar