Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce dakarun soji na musamman sun kashe ‘yan ta’adda tara a wasu yankunan da ke a karamar hukumar Giwa a jihar.
A cikin sanarwar da kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida, Mista Samuel Aruwan, ya fitar a yau Alhamis, ya ce dakarun sun samu wannan nasarar ne bayan sun tarwatsa wani sansaninsu da ke a Rafin Sarki.
- Zulum Ya Gabatar Da N234.8b A Matsayin Kasafin 2023 Ga Majalisar Dokokin Borno
- Qatar 2022: Tutar Afirka Na Ke Son Dagawa Bata Larabawa Kadai Ba – Kocin Morocco
Aruwan, ya cewa dakarun sun kuma kama biyar daga sauran da suka arce, ya kara da cewa, dakarun sun kuma tarwatsa wani sansaninsu da ke a dajin Galadimawa, inda suka kama ‘yan ta’adda hudu.
A cewar Aruwan, dakarun sun kuma kubutar da mata da yawa da yara da ‘yan ta’addar suka sace, tare da kwace bindigu kirar gida, albarusai, kakin soji da sauransu.
Gwamnatin jihar ta yi kira ga daukacin ‘yan jihar da su ci gaba da bayar da goyon bayansu wajen bayar da sahihin bayanai a kan maboyar ‘yan ta’adda ta hanyar kiran wadannan lambobin wayar kamar haka: 09034000060, 08170189999.