Jama’a barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na Taskira, shafin da ke zakulo muku batutuwa da suka shafi al’umma na bangarori daban-daban, wadanda suka hadar da rayuwar matasa, soyayya, rayuwar yau da kullum, zamantakewar aure, da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne danagen da irin matsalolin da wasu matan ke tsintar kansu a ciki, na dangane da karin aure da wasu Mazan ke yi ba tare da sun sani ba. A lokutan baya kadan da suka shude, maza sun sha yayin tafiye-tafiye zuwa wani gari da zummar zuwa wajen aiki, wanda daga bisani matan nasu sai su ji zancen ya canja ta yadda labari zai iso musu na mijinsu ya kara aure, wata ma sai Amaryar ta tara yara tukunna za ta sani.
Sai dai kuma a yanzu sabon salon da wasu mazan suka shigo da shi shi ne; karin aure ba tare da matar ta sani ba sai ana i-gobe, ko bayan daurin aure, ko kuma a ranar da Amarya za ta tare, a ganinsu yin hakan shi ne dai-dai domin muddin suka sanar da wuri za ta iya hana kara auren.
A nawa tunanin yin hakan ba daidai ba ne, domin hakan zai iya janyo zubda mutunci, da rashin girmamawa, da rashin zaman lafiya, da rashin jituwa, da rashin kulawa da dai sauransu, domin idan wata ta iya jure hakan, wata ba za ta iya jurewa ba, dalilin hakan zai sa girman mijin da kimarsa ya zube kasa har ta farfadi abin da ita kanta ba ta taba tunanin za ta iya fada masa ba, wanda ya shafi cin mutunci. Yana da kyau masu hakan su kara sani muddin wadanda sukai wa hakan ba masu ta da hankali bane, ba masu ziyartar bokaye da malamai dan raba aure ba ne, to sun shiga hakkinsu.
Domin kuwa duk wanda aka yi wa ‘yarsa ko kanwarsa ko yayarsa haka, ba zai taba amincewa ba, dan ba zai taba goyon bayan namijin da ya yi mata hakan ba, hasali ma da shi za a hadu a fadi kuskuren mijin.
Da yawan maza na kallon yin hakan tamkar shi ne masalaha da samun zaman lafiya, da kwanciyar hankali, da kuma samun damar yin karin auren, ba tare da ya ruguje ba. Abin dubawa a nan shi ne; ko da a ce akwai Mata marasa mutuncin da in an sanar da su za su yi kokarin raba auren, to amma ai ba dukka aka taru aka zama daya ba, kamar yadda su ma mazan ba dukka suka taru suka zama daya ba, akwai mazan da suke sanar da matansu cikin lumana kuma a yi auren su zauna lafiya.
Toh! ba za a ce kaf! Matan da maza ke zaune da su a gidajensu an rasa tagari ba, domin wani ba wai ya rasa duk abin da yake bukata na tarbiyya da kyautatawa, da kulawa, a wajen matarsa ne ke sawa ya kara auren ba. Wasu Mazan na karawa ne domin bukatuwarsu da hakan, ko dan tara yara masu yawa ko wani dalili daban, ba wai dan ba ta iya komai ba, kuma ba dan babu tarbiyyar ba.
Amma kuma duk da nagartar da wasu matan suke da shi, wasu mazan na watsi da sanin hakan su shiga sahun yayin da aka shigo da shi na karin auren sirri. Wanda kuma sam! ba tsoron bacin ran matar ke sa su hakan ba, ba kuma shayi ba ne, kawai shiga yayi ne da idan wani ya yi shi ma sai ya yi, idan kuwa bai yi ba to ba zai ji dadi ba. Yana da kyau Maza su gyara wannan dabi’ar wajen rashin sanar da matansu zancen karin aure da wuri, ko da a ce mace ranta zai baci ya kamata ka sanar mata da wuri, domin zama ne kuka yi shi tsahon shekaru, me cike da soyayya ba wai sabanin hakan ba.
Yana da kyau maza su san dabi’un matansu wanne abu ne za su iya yinsa, wanne ne ba za su iya ba, ko dan gudun yi musu kudin goro tsakanin nagari da wadanda ba nagari ba. Yana da kyau maza su san hanyoyin da za su rinka bi domin sanar da matansu zancen karin aure, su tunano kyawawan kalaman da suka mance na baya da suka rinka yi musu tun kafin aure, wanda ya sa har mace ta amince da aurenka.
Kalamai kala-kala ne ba wai ina nufin kalamai na lokutan baya da suka wuce na kuruciya ba, za a tsaya ne a yi nazarin hanyoyin da za a bi wajen furta wa uwargida abin da ke zuciya na zancen karin aure, ta yadda ba za a furta shi kai tsaye ba, sai an bi ta hanyoyin da furucin zai zo a kan gaba, tare da yin nuni da wasu kyawawan dabi’u na uwargida wanda take da su, gami da lallashi me cike da tausayawa, tare da janta a jiki, idan kalaman kuruciyar ma zai sa ta farin ciki duk a hada mata da su.
Kar a saka jin kai ko jiji da kai da girman kan an fi karfin ayi mata haka, a rinka tuna farkon aure ko na ce kafin aure ya al’amarin ya kasance. Wannan a takaice kenan.
Dalilin hakan ya sa wannan shafi ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da irin wannan matsalar “ko haka addini ya ce a yi, ko yayi da sabon salo ne da wasu mazan suka zo da shi kawai?, ko me yake janyo hakan?, wanne irin matsalolin hakan ke iya haifarwa?, idan an tsinci kai ciki wanne mataki za a dauka?, ta wacce hanya za a magance matsalar?”. Ga dai ra’ayoyin nasu kashi na farko, domin saboda muhimmancin abin za mu ci gaba a mako mai zuwa.
Fadila Lamido daga Kaduna:
Wannan shi ne daya daga cikin rashin adalcin da maza suke yi wa mata. Domin kuwa babu wadda ya cancanta ya fara sanin neman auren namiji sama da matar shi, ba ka da hujja ko dalilin rufe mata, idan kuwa kana tsoron ka da ta tayar maka da hankali ne to ba ka cancanci kara auren ba. Tun tana ita daya ma ba ka iya yi mata adalci ba bare ka karo wata.
Maza suna mantawa da wani abu guda daya idan sun so kara aure. Sai idonsu ya rufe su manta ma cewa soyayya ce ta hada su da wannan matar ta cikin gida ba kiyayya ba. sai su mai da ta cikin gidan tamkar wata makiyiyar su, wadda hakan ba daidai bane.
Aure wani abu ne wanda Allah ya tsara shi tsakanin mace da namiji. Akwai zama na kauna cikin kwanciyar hankali, tare da tausayawa da jin kai. Allah shi ne ya bawa maza damar su auri mace sama da daya, kuma shi ne dai ya halastawa mace yin kishin mijinta.
Kenan dan mace ta nuna kishin mijinta yayin da ya sanar mata da karin aure ba haramun bane. Hakika babu macen da mijinta zai sanar mata da karin aure ta ce ta ji farin ciki duk imaninta, Ina son maza su lura da wani abu guda daya: sai abun da ake so sannan ake nuna kishi a kanshi. Me yasa nuna soyayya ya ke zama kiyayya a daidai irin wannan lokacin?, ka fi son idan ka sanar da ita ta yi murna ne?, ashe ba sonka ta ke ba kenan. Idan har akwai soyayya dole kishi ya kama ta, girman kishin da za ta nuna a irin wannan lokacin shi ne adadin kyaunar da take maka. Idan ko har ka kasa fahimtarta ta hanyar kasa yi mata uzuri baka yi mata adalci ba, idan akwai tausayi da jin kai na matar ka a zuciyar ka kamata yayi ka daura damarar tausan zuciyanta, ba wai ka maida ta tamkar wata abokiyar hamayya ba.
Idan akwai adalci kamata yayi ka kwatanta abun a kanka, alal misali ace an bawa mace damar auren namiji sama da daya yaya za k jji a irin wannan lokacin? dole akwai kishi. Dan haka kamata yayi ka jaw tta a jiki fiye da baya. Ka tabbatar mata da cewa har yanzun tana da daraja a gurinka, har ta ji a ranta ta gamsu.
Kowa ya san cewa mace tana da rauni, me yasa idan namiji ya tashi kara aure baya tuna rauninta? Sai a yanke mata hukunci da mara adalci kawai alhalin baka biyo mata ta hanyar da ya dace ba, sai a watsar da soyayyar da a ka yi a baya ka ga tamkar ma ba a taba yi ba.
Irin wannan shi ne ya ke tunzura wasu matan har su aikata abun da bai dace ba, da an bude baki sai dai ka ji an ce ta cika kishi, ita kanta wannan kalmar tana tunzura mace. Kishi halitta ne, kuma ita kanta wadda za ta shigo din da kishinta take shigowa bare wadda take ciki. Dan haka ita wadda take cikin gidan ita ya kamata a jajirce wajen tausan zuciyarta ba tare da kyara ko hantara ba, idan har ba ka da lokacin rarrashinta to baka cancanci auren mace sama da daya ba. Na kan ji wasu mazan suna cewa: wai abun da ya sa ba sa gayawa mace za su kara aure wai za ta shiga malaimai ne ta hana auren duk namiji da ya ke kan irin wannan ra’ayin; kenan a gurinshi matar ta samo tarbiyar rashin dogaro da Allah, in da ka yarda da Allah wannan ba zai zama hujja ba. Domin babu wani me yi sai Allah, babu wani wadda ya Isa ya dakatar da abun da Allah ya rubuta shi a cikin Littafinka. Idan ka ga bai faru ba ba a rubuta maka shi ba ne, ko kuma lokacin faruwar shi bai yi ba.
Dan haka boye kara auren da maza suke yi rashin adalci ne kawai. Kuma tun anan gurin suke haddasa hargitsi da rashin kwanciyar hankali, amman ba dukka aka taru aka zama daya ba akwai wasu tsuraron maza masu adalci wadanda za a ga sun daraja uwar gidansu.
Kuma irin wannan ko amaryar ta shigo an fi zama lafiya saboda mijin bai raina matar shi ba wata ma ba za ta zo ta rainata ba. Idan ni ce hakan ta faru a ce sai ranar auren ko ana gobe ya sanar min, gaskiya rabuwa da shi shi ne; abin da zai fi min alheri, domin babu tausayi, jinkai, anan gurin. Mamakin munafurcin kawai ya isa ya buga zuciyata, ba zan iya zaman munafurci ba, yadda na bude maka gaskiyata kai ma ka bude min taka duk dacinta, idan ko har aka tursasa min ci gaba da zama da kai ba za ka same ni kamar baya ba, domin kuwa ka riga ka baro gini tun rani.
Shawarata ga maza su zama jajirtattu ba ragwaye ba yayin da suka tashi kara aure, kuma su daina mantawa da soyayyar da aka yi a baya; su bawa ta cikin gidan cikakkiyar kulawa domin kwantar da kishinta ba tare da kyara ko hantara ba.
A irin wannan lokacin uwar gidan na cikin tsananin son kulawa ne, kuma kulawarka za ta fi so sama dana kowa aduniya, domin da kai ta saba, idan har ba ka ja ta a jiki ba za ta fita ta je inda za a iya bata gurguwar sharawa. Idan da hali kar ma ka yadda wani ya ji tsakaninku, ku kashe ku rufe babu wadda ya ji bare ya gani, lankwasa mace yana da matukar sauki ga namiji me wayo. Sannan namji ya sa ranshi cewa babu wadda ya isa ya dakarta da abin da Allah ya hukunta.
Ayshatul Humaira Ibrahim (Ayshe) daga Jihar Kano:
Abin da ya sa mazan yanzu suke haka; suna tsoron sanar da matar ne idan za su kara aure. Dan wata macen babu abin da ba za ta iya ba idan ta ji mijinta zai kara aure. Nan da nan za ta tashi a tsaye Neman farraku, sai ki ga namiji yayi ta neman aure karshe yana wargajewa,to shiyasa suma sai suka canza taku suke boyewa matan har sai an daura masu aure, wasu kuma sai abu ya zo daf! sai su sanar musu.
Musbahu Muhammad Gorondutse Kano:
Wasu Mazan suna tsoron masifar matansu shiyasa suke boyewa sai bikin ya zo sannan suke fada musu, amma hakan kuskure ne A al’ada da kuma addini. Tsabar tsoro ne yake saka wasu Mazan yin haka. Matsala kam dole ta faru tunda an yi abu a boye kuma ya fito fili kuma mace tsaf za ta kalli mijin ta kira shi munafiki.
Idan mutum zai kara aure ya fito fili ya sanar da matarsa ta hanya me kyau da daddadan lafazi, sannan ya sanar da ita yana sonta yana kaunarta, Allah ne ya kaddara kuma ya halatta. Masu yi su ji tsoron Allah a zamantakewar su, su yi adalci sannan su yi kyakkyawar mu’amala da bayani a tsakaninsu da matayensu.
Mako mai zuwa za mu kawo muku ci gaban fashin bakin da ma’abota shafin Taskira suka yi a kan wannan batu.