ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin: An Samu Karuwar Adadin Cibiyoyin Cajin Ababen Hawa Masu Amfani Da Lantarki

by CMG Hausa
4 years ago
Sin

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Alkaluman kididdiga sun nuna cewa, a shekarar bana, adadin cibiyoyin cajin ababen hawa masu amfani da lantarki na karuwa cikin sauri a sassan kasar Sin. Karuwar wuraren cajin na lantarki ko EVs, ya samar da dama ta biyan bukatun al’ummar kasar, wadanda ake amfani da nau’o’in ababen hawan dake amfani da lantarki.

Rahotanni daga hadakar kungiyoyin dake rajin bunkasa samar da na’urorin cajin ababen hawa masu aiki da lantarki ko EVCIPA, sun ce ya zuwa karshen watan Nuwamba, adadin irin wadannan cibiyoyin caji sun kai kusan miliyan 4.95, wanda hakan ke nuna karuwar kaso 107.5 bisa dari idan an kwatanta da na makamancin lokacin na bara. Kaza lika tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamban bana, an kara kimanin irin wadannan wurare na caji har miliyan 2.33 a sassan kasar ta Sin.

  • Sin Ta Tallafawa Wani Asibitin Kasar Uganda Da Kayan Aiki

Bisa jimilla, adadin wuraren cajin sun ninka wadanda ake da su a shekarar bara, kuma cibiyoyin cajin na sassa masu zaman kan su, su ma sun ninka har sau 4, cikin watanni 11 na farkon shekarar nan, idan an kwatanta da karuwar su a wasanni 11 na shekarar.

ADVERTISEMENT

Ana alakanta wannan babban ci gaba da aka samu, da fadadar sashen amfani da ababen hawa masu aiki da sabbin makamashi na kasar Sin. Daga watan Janairu zuwa Nuwamba, adadin ababen hawa masu aiki da lantarki da aka saya a Sin, sun kai miliyan 6.07, adadin da ya ninka na sabbin cibiyoyin cajin da aka samar a tsakanin wa’adin har sau 2.6, wanda hakan ke nuni ga cewa, ana cimma bukatar saurin bunkasar sashen kamar yadda ake fata. (Saminu Alhassan)

Sin
CMG Hausa
+ postsBio
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugabannin Kasashen Duniya Sun Yi Wa Sin Fatan Alheri A Sabuwar Shekara
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    San Francisco sabon mafarin hadin gwiwar Sin da Amurka ne
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Xi Ya Halarci Kwaya-Kwaryan Taron Shugabannin Mambobin APEC
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Jagororin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
Hulda Tsakanin Sin Da Kasashen Yankin Gulf Za Ta Samu Sabon Kuzari

Hulda Tsakanin Sin Da Kasashen Yankin Gulf Za Ta Samu Sabon Kuzari

LABARAI MASU NASABA

Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.