Gobara ta kone a wani dakin ajiyar kaya da ke kan titin Idumagbo a unguwar Obun Eko da ke jihar Legas.
Daraktar hukumar kashe gobara na jihar Legas, Margaret Adeseye, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
Daraktan ya bayyana cewa hukumar zata fara gudanar da bincike kan musabbabin faruwar lamarin, inda ya kara da cewa ba a samu rahoton mutuwa ko jikkata a lamarin ba.
Adeseye ya ce, “A halin yanzu hukumar kashe gobara ta jihar Legas ta kashe gobara a wuri mai lamba 34, Idumagbo Avenue, Obun Eko, Legas.
“Hukumar wadda aka sanar da ita da karfe 12:31 na daren ranar Litinin, ta hada kai da hukumomin kashe gobara na Ebute Elefun da Oniru domin shawo kan gobarar da ta tashi a gidan mai hawa uku.
“Gobarar wacce ta tashi a wani dakin ajiyar kaya da ke hawa na uku na ginin wanda ke dauke da tawul, shimfidar gado, tudin kaset da dai sauransu, tare da wani bankin kasuwanci a kasa.
“Jami’an kashe gobara na Legas tare da hadin gwiwar hukumomi sun yi nasarar shawo kan gobarar zuwa hawa na ukun da kuma gidajen da ta bazu da ceto bankin da sauran benaye da kuma sauran gine-gine.
“Babu wani rahoton samun rauni ko mutuwa kamar yadda bincike ya tabbatar.”