Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa ba za su yi nadamar zabarsa a 2023 ba.
Da yake jawabi a Kaduna a ranar Talata a taron shiyyar Arewa maso Yamma, dan takarar shugaban kasar ya ce, “Ina so na tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa zabe na a matsayin shugaban kasar nan zai kawo karshen matsalolin da ‘yan kasar nan ke fuskanta.”
- ‘Yansanda Na Bincike Kan Cire Idon Wani Almajiri A Bauchi
- 2023: INEC Ta Gargadi Masu Sayar Da Katin Zabensu Ga ‘Yan Siyasa
Ya kuma gargadi duk masu tayar da zaune tsaye da su nemi maboya, yana mai tabbatar da cewa duk wanda ba zai rungumi lafiya da hadin kai da ci gaban kasa ba, ba zai samu sassau daga shi ba.
Ya kara da cewa kalubalen tsaro da ake fuskanta yanzu zai zama tarihi kuma ‘yan Nijeriya na iya gudanar da harkokinsu na yau da kullun.
Ya bayyana cewa, “Gwamnatina za ta yi duk mai yiwuwa wajen samar da ayyukan yi, ta yadda matasanmu za su yi maganin halin da suke ciki. Za a ba da duk wata dama ta bai wa manomanmu yanayin da za su iya komawa gonakinsu da abubuwan da suka dace don bunkasa noma a kowane bangare na kasar nan”.
Ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su shirya musu katin zabe, yana mai cewa su shirya zaben APC a zaben 2023, don ita mafitar ‘yan Nijeriya.
Tun da farko Gwamna Nasir El-Rufai ya godewa al’ummar yankin Arewa maso Yamma da suka zo Kaduna domin gudanar da gangamin, ya kuma umarce su da su tabbatar sun zabi jam’iyyar APC a dukkan matakai a zaben badi.