Magoya bayan dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP reshen jihar Ribas sun sake nanata martanin su ga gwamnan jihar Nyesom Ezenwo Wike cewa, sun fi shi yin biyayya ga jam’iyyarsu ta PDP.Â
Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben Atiku a jihar, Dakta Abiye Sekibo ya bayyana hakan a wata tattaunawa da kwamitin ya gudanar a garin Fatakwal, inda ya ce, akasarinsu da aka hana tikitin tsaya wa takarar kujerar gwamna a PDP a jihar ba su sauya sheka zuwa wata jam’iyyar ba kuma ba su fice daga cikinta ba.
Sekibo ya ci gaba da cewa, duk da cewar an hana musu tikitin tsaya wa takarar kujerar gwamna a jihar, amma mun ci gaba da tura PDP gaba a jihar da karfin mu da kuma hawayen mu, inda yace, wannan ya nuna cewa, mu masu biyayya ne ga PDP, amma kuma mai ya sa shi Wike yake yin hakan a jihar.
Shi ma shugaban kwamitin yakin neman zaben Atiku a jihar, sanata Lee Maeba ya ce, magoya bayan takarar Atiku a jihar sun shafe shekaru suna yin hakan.
Maeba ya ce, wadannan magoya bayan sune ke dauke da cikakken jinin PDP a cikin jikinsu da na iyalansu, inda ya yi kira ga mahukunta a jihar cewa hare-haren da ake kai wa magoya bayan Atiku a jihar ya isa haka.
Ya kuma nuna takaicinsa akan yadda Wike ya ki fito wa ya yi Allah wadai akan harin da wasu ‘yan bangar siyasa suka kai a gidansa da ke a garin Fatakwal a makon da ya gabata.