Kungiyar Dillalan Man Fetur Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (IPMAN) a Jihar Ogun, ta yi barazanar rufe dukkanin gidajen man da ke fadin jihar sakamakon wa’adin da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), ta bai wa ‘yan kasuwa na kawo karshen matsalar karancin man fetur.
A makon nan ne dai Hukumar DSS ta bai wa Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) da ‘yan kasuwar man fetur wa’adin sa’o’i 48 da su samar da man fetur a fadin Nijeriya sakamakon karancin man fetur da ake fama da shi.
- 2023: Mallakar Katin Zabe Ya Fi Mallakar Takardun Makaranta A Wannan Lokacin -Gumi
- Bikin Kirisimeti: Wanda Takardun Fasfonsa Ya Kare Zai Iya Dawo Wa Gida – Gwamnati
Amma yayin da take mayar da martani ga wa’adin hukumar ta DSS, IPMAN ta ce irin wannan manufar ta gaza “saboda tunanin ta tare da ‘yan kasuwa na gaskiya wadanda ba sa samun kayayyaki daga ma’ajiyar gwamnati don sayarwa a farashin da gwamnati ta amince.”
A wata sanarwa da shugaban kungiyar a Ogun Femi Adelaja ya fitar, ya bukaci hukumar da ta bi sahun wadanda ke wahalar da ‘yan kungiyar ta IPMAN.
Adelaja ya bayyana matakin da DSS ta dauka kan karancin man fetur a matsayin wata dabara ta gwamnati da ta gaza wajen gudanar da ayyukanta da ya kamata ta kuma zabi ta cuzgunawa ‘yan kasuwa a ko’ina da sunan tabbatar da tsaron kasa.
Don haka kungiyar ta gargadi hukumar DSS da ta sauya matsayinta na matsa wa IPMAN lamba, tare da bai wa ‘yan Nijeriya hakuri kan matakin da ta dauka.