An samu tashin hankali a yankin Aladja da ke karamar hukumar Udu a Jihar Delta sakamakon tarzoma da ‘yan daba suka tayar a wajen taron jam’iyyar APC, wanda tsohon shugaban matasa jam’iyyar PDP, Obaro Matthew Jagogo ya shirya.
‘Yan daban sun afka wajen taron, suka ce suna bin Jagogo bashin dubu dari hudu.
- CMG Ya Fitar Da Shirin “Shawarar Daukar Matakin Neman Bunkasuwa Na 2022” A Shafin Yanar Gizo
- A Kara Tsaurara Tsaro A Hanyoyinmu
Sun tarwatsa taron tare da korar duk wadanda suka halarci taron.
Kwamared Jagogo ya shirya taron ne da nufin ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC saboda wasu dalilai.
Ana sa ran zuwan manyan ‘yan siyasa irinsu Collins Egbetamah, dan takarar majalisar wakilai, Keston Okoro da Williki a wajen taron a lokacin da ‘yan daban suka afkawa unguwar da ke Ekregwar a yankin Aladja.
Da aka tuntubi Shugaban Jam’iyyar APC na Aladja, Mista Abeyi Lucky wanda ke wurin yayin da abin ya faru, ya ce, “Abin da ba mu yi tsammani ba ne kawai”.
Har zuwa lokacin da ake wannan rahoto, ana fargabar cewa lamarin na iya haifar da rikici tsakanin jam’iyyar APC da ‘yan adawa a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp