Dakarun rundunar ‘Operation Forest Sanity’ sun gudanar da aikin share fage a sansanin ‘yan bindiga da aka gano a kauyen Kidandan da ke karamar hukumar Giwa a Jihar Kaduna, inda suka kashe ‘yan ta’adda biyu tare da kwato makamai da babura.
Daraktan yada labarai na rundunar, Manjo-Janar Musa Danmadami, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce sojojin sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda biyu, sun kwato bindiga kirar AK 47 guda daya da harsashi 52 masu dango 7.62mm da babura biyar da wayoyin hannu uku.
- Croatia Ta Lallasa Morocco A Gasar Cin Kofin Duniya A Qatar
- Manyan Kwamandojin Boko Haram 4 Sun Mika Wuya Ga Sojoji A Borno
A wannan rana, sojojin sun kuma gudanar da aikin share fage a kan hanyar Kaduna zuwa Zaria zuwa Galadimawa inda suka kai wa ‘yan ta’adda hari a sansanoninsu.
Ya ce ‘yan bindigar sun gudu ne bayan da suka ga sojoji sun lalata sansanoni da dama a yankin, sun kwato bindigogin guda uku da babura tara da kakin soja guda biyu, da dai sauransu.