Rundunar ‘yansandan Jihar Kwara ta kafa wasu matakan tsaro da nufin tabbatar da an yi bukukuwan Kirsimeti a jihar cikin kwanciyar hankali.
Wata sanarwa da kakakin ‘yan sandan rundunar ‘yansandan jihar, SP Okasanmi Ajayi, ya fitar a Ilorin ranar Talata, ta ce matakan sun hada da dumbin tura mutane da kayan aiki a ciki da wajen cibiyoyin gwamnati da kuma dukkan kadarorin gwamnati.
- Kan ‘Yan Majalisar Jigawa Ya Rabu Kan Batun Tsige Shugaban Karamar Hukuma
- 2023: Ba Zamu Hade Da Kowace Jam’iyya Ba – Idahosa
A cewar Okasanmi, za a kuma aike da ‘yan sintiri don dakile masu tayar da kayar baya a motoci da kafa, don yi bincike, da kuma ci gaba da kai hare-hare kan bata gari.
Ya kuma bai wa mutanen jihar tabbacin a shirye hukumar take na tabbatar da gudanar da bukukuwan Kirsimeti cikin lumana da jin dadi a fadin jihar.
Rundunar ta bukaci hadin kai da fahimtar kowa da kowa wajen tabbatar da matakan tsaro.
Kakakin ya kara da cewa, “Ana iya yin hakan ta hanyar kai rahoton duk wani motsi da ake zargi ga ‘yansanda tare da ba da bayanai a kowane lokaci.”
Ya ce kwamishinan ‘yansanda, Paul Odama, yayin da yake taya mabiya addinin kirista a jihar murna, ya umarce su da su yi bikin tsaka-tsaki ke yi.
“Hakan za su iya yi ta hanyar guje wa tukin ganganci, bin duk dokokin hanya da kuma yin addu’a don dorewar zaman lafiya a jihar,” in ji shi.