Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano a ranar Alhamis ta tabbatar da Mohammed Sani Abacha a matsayin zababben dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Jihar Kano.
Leadership Hausa ta rawaito cewa alkalin kotun mai shari’a A.M Liman a wani hukunci da ya yanke a yammacin ranar Alhamis ya soke zaben fidda gwanin da ya samar da Sadik Aminu Wali a matsayin dan takarar gwamnan Jihar Kano a jam’iyyar PDP tare da umartar INEC da ta maye sunansa na Mohammed Abacha.
- ‘Yansanda Sun Cafke Mutum 9 Da Ake Zargi Da Kai Wa Tawagar Atiku Hari A Borno
- 2023: Buhari Ya Gana Da Tinubu A Villa
An yanke hukuncin ne da misalin karfe 12:00 na rana a yau amma daga baya aka canza lokacin zuwa karfe 4:00 na yamma.
Kotun ta amince da dukkan hujojjin wanda ya shigar da karar.
Mohammed Abacha ne ya shigar da karar yayin da wadanda ake kara su ne Sadik Aminu Wali, INEC, da kuma jam’iyyar PDP a jihar.