Mayar da safga ko ayyukan hutu zuwa safgar da zai kawo maka samun kudi ko budi ba abu ne da ke da matukar amfani kawai ba ne har da jindadi yake sakawa.
Ga wanda ke da muradin zama ‘on air personality (OAP)’ kuma ba ya son barin ayyukansa na yau da kullum da ke kawo mai samu, fara Radiyon Intanet na daya daga cikin mafita.
- Shugaban Kamfanin Jirgin Sama Na Max Air Ya Rasu
- Kirisimeti: Gwamnatin Bauchi Ta Raba Kayan Abincin Miliyan 145 Ga KiristociÂ
Ya na da matukar riba sosai kuma Yana da saka nishadi a zukatan masu yin ta kuma akwai matukar riba sosai ga mutumin da ke da bukatar jari Kadan don farawa.
Kuma Sana’a ce wacce za a iya bunkasa shi don zama manyan tushen samun kudi musamman idan aka kula sosai, ba Kaman Radiyon duniya ba, ba Ka da bukatar samun lasisi don yada shirye shirye kuma idan tashar ka zai rika saka haajar kasuwancin waka to zai iya bukatar lasisi, in ba haka ba tashar Ka zai zama kashi kashi Kaman a matsayin bangaren mai zaman Kansa kuma hukuma ba za ta yarda dashi ba.
Radiyon Intanet na da kamaceceniya da Radiyon gargajiya,sai dai don ba amfanin masu watsawa tunda ana Watsa shirye shiryen Shi ta Intanet kuma masu sauraro BA su iyakance Akan yankin yanki Daya BA.ta hanyar Radiyon Intanet,duniya na dunkulewa wato raguwa ya dawo kamar kauyen da ke da masu sauraro da wurin kasuwa.
Yayin Fara Intanet Radiyo,za Ka bukaci dakin shiru, laptop da hadin Intanet da makirufo mai kyau da sauke amon belun kunne wato noise cancelling headphones.kuma za Ka bukaci Yanar Gizo don bawa masu sauraro daman Kara fahimta KO Sani Akan tashar ka.