An gurfanar da wani mutum mai suna Idris Suleiman a gaban wata babbar kotun jihar Kebbi, bisa laifin kashe wata matar aure da diyarta ‘yar shekara hudu a unguwar Kamfanin Labana da ke cikin Birnin Kebbi.
Wanda ake tuhuma dai Idris Suleiman dan asalin Jamhuriyar Nijar ne ke fuskantar tuhuma biyu na aikata laifin kisan kai da ake iya yanke hukuncin kisa a karkashin sashe na 191 (a) na dokar Penal Code na jihar Kebbi 2021.
Wakilinmu ya tuna cewa wanda ake zargin ya daba wa matar wuka ne har lahira sannan ya bugi kan karamar yarinyar a kan fale-falen dakin mahaifiyar wanda ya yi sanadin mutuwarta ita ma.
Da take gurfanar da wanda ake zargin a gaban mai shari’a Suleiman Ambursa kuma shi ne babban jojin jihar Kebbi, Darakta mai shigar da kara ta ma’aikatar shari’a a Jihar (DPP), Barista A’isha Abbas tare da Barista Zainab Jabbo da kuma Barista Aminu Diri sun shaida wa kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne watanin biyu zuwa na uku da suka gabata a cikin hurumin wannan kotun.
Domin tabbatar da aikata laifin , DPP ta kira shaidu shida tare da gabatar da shaidarsu a gaban kotun a karkashin mai shari’a Sulieman Muhammad Ambursa da ke kotu ta daya a Birnin Kebbi.
Bayan gabatar da shaidar shaidun, lauyoyin masu gabatar da kara sun rufe karar nasu.
Lauyoyin da ake kariyar Wanda ake tuhuma a cikin karar mai lamaba KB/HC/27C/2022, Barista Alhassan Salisu-Muhammad, wanda kuma shi ne Shugaban ofishin Lauyoyin masu kare marasa galihu a Jihar Kebbi tare da wasu lauyoyin da suka riga sun hada da; Barista Iliyasu Adamu da Mrs Afu M. A. suka bude nasu kariya kuma sun tabbatar wa da kotun cewa sun kammala ba da kariyar su a gaban kotun.
Haka kuma Lauyoyin da ke kare wadanda ake tuhuma sun kira shaida guda daya (wanda ake tuhuma) don tabbatar da kare su tare da rufe ba da kariyar su nan take.
Daga nan, Lauyoyin masu gabatar da kara da kuma masu kare wanda ake tuhuma sun nemi izinin kotun ta dage shari’ar zuwa ranar 30 ga watan Yuni, don gabatar da dukkan hujojin su da kuma yin mahawara kan hujojin a gaban kotun.
Alkalin kotun dai, ya dage sauraren karar zuwa ranar 30 ga watan Yuni domin amincewa da rubutaccen hujojin na lauyoyin bangare biyu.