Hukumomin Kasar Saudiyya sun hana sayar da kayan wasan yara da tufafi mai Launin gajimare Kan zargin cewa suna tallata halayyar luwadi ga al’umma.
BBC Hausa ta rahoto cewa tuni Hukumomi a kasar Saudiyya suka fara kwace kayayyakin da ta haramta.
Cikin abubuwan da aka fara kwace wa sun hada da basilla ta tamke gashin mata da riguna samfurin t-shirt da huluna da kuma gidajen ajiyar fensira.
Hukumar ta Jaddada cewa, tufafi mai launin gajimare ya sabawa launin tufafi da addinin musulunci ya yarda ayi aiki dashi, Kuma wadannan Kayan da aka haramta suna taimaka wa wajen tallata halayyar luwadi ga matasan kasar.
Don haka, Hukumomin sun gargadi masu sayar da kayan cewa za su fuskanci hukunci idan aka sake samunsu da kayan a shagunansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp