Ranar 23 ga wata, aka kammala kashi na farko na aikin ginin yankin raya masana’antu na PK24 da kamfanin gina tashoshin jiragen ruwa na kasar Sin na CHEC ya gudanar a kasar Cote d’Ivoire.
A jawabin da ya gabatar yayin bikin kammala aikin, firaministan kasar Cote d’Ivoire Patrick Achi Jérôme ya bayyana cewa, wannan babban aikin zai taimaka wajen kyautata hanyar raya tattalin arzikin kasar, da farfado da masana’antun kasar. Ya kuma karfafawa kamfanoni gwiwa, da su zauna da gindinsu a yankin raya masana’antu na PK24, a kokarin bayar da gudummawa ga ci gaban tattalin arziki da samar da guraben ayyukan yi ga matasan kasar.
A nasa bangaren kuma, Souleymane Diarrassouba, ministan cinikyayya da masana’antun kasar Cote d’Ivoire ya ce, kamfanin CHEC ya haye dimbin wahalhalu yayin gudanar da aikin, kafin ya gama aikin gina wannan yankin raya masana’antu na zamani da ke da karfin takara sosai.
Haka kuma, yayin da babban manajan yankin yammacin Afirka na kamfanin CHEC Wang Guangsheng ke zantawa da wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin, ya bayyana cewa, bayan kammala aikin, za a jawo karin kamfanoni da su zuba jari, ta yadda za a samar da dimbin guraben ayyukan yi ga mazauna wurin.
Kashi na farko na yankin raya masana’atu na PK24, yana arewa maso yammacin birnin Abidjan, babban birnin kasar Cote d’Ivoire, wanda fadinsa ya kai kadada 127, kuma an fara aikin gina shi a ranar 1 ga watan Fabrairu na shekarar 2020.(Kande Gao)