Amurka ta sanar da janye jiki daga kasar Syria tun shekaru 4 da suka wuce, amma har zuwa yanzu, wasu sojojin kasar Amurka 900 na ci gaba da kasancewa a arewacin kasar.
A cewar kasar Amurka, dalilin da ya sa hakan shi ne magance farfadowar kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi a Syria. Amma a cewar gwamnatin kasar Syria, wadannan sojoji na kasar Amurka na kwatan danyen mai, da alkama, da sauran albarkatu iri-iri na kasar.
Hakika wani babban aiki na wadannan sojojin kasar Amurka, shi ne samar da goyon baya ga dakarun kasar Syria masu kin jinin gwamnati, inda ake ba su taimako wajen mallakar mahakan mai da iskar gas dake arewa maso gabashin kasar, da jigilar mai zuwa kasar Iraki domin sayar da shi.
A cewar gwamnatin kasar Syria, sojojin Amurka da dakaru masu kin jinin gwamnati, sun riga sun haddasa mata asarar da ta kai dalar Amukra biliyan 25.9. Kana a watanni 6 na farko na shekarar bana, sojojin Amurka da dakarun da suke samun goyon baya daga wajensu, sun kwaci fiye da kaso 80 na danyen man da aka haka a kasar Syria.
Ban da wannan kuma, kasar Amurka da wasu kawayenta na ci gaba da saka takunkumi kan kasar Syria, ko da yake kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya bai samar da iznin yin haka ba. Wannan takunkumi ya shafi bangarorin tattalin arzikin kasar Syira masu muhimmanci, da suka hada da danyen mai, da wutar lantarki, da cinikayya, da dai sauransu, lamarin da ya haddasa raguwar kudin shigar da jama’ar kasar suke samu, da hauhawar farashin kaya.
Zuwa yanzu kashi 90% na al’ummar kasar sun tsunduma cikin kangin talauci. Kana daga shekarar 2019 har zuwa yanzu, matsakaicin farashin kayayyaki na kasar ya karu da kashi 800%. Kuma wani abun takaici shi ne, Amurka da kawayenta sun ce dalilin da ya sa suka kakaba wa kasar Syria takunkumi shi ne kare jama’ar kasar.
Hakika Amurka ba za ta daina yin tasiri a kasar Syria ba. Ta hanyar raunana gwamnatin Syria da takunkumi, da taimakawa dakaru masu kin jinin gwamnati da damar shawo kan albarkatun danyen mai da iskar gas, kasar Amurka na ci gaba da kokarin neman hambarar da gwamnatin kasar. Ko da yake tana gudanar da ayyukan fakewa da kalmomin “dimokuradiya”, da “hakkin dan Adam”, da “tsaro”, da “zaman lafiya”. Amma kar mu manta, cikin shekaru 20 da suka wuce, matakan da kasar Amurka ta dauka a kasashe da yankuna 85, sun haddasa asarar rayukan mutane kimanin dubu 900, da rashin matsugunan mutane fiye da miliyan 38.
Tutocin “Dimokuradiyya”, da “Hakkin dan Adam” da kasar Amurka ta rike sun riga sun lallata sosai. Anya kasar za ta iya ci gaba da fakewa da su? (Bello Wang)