Bankin raya kasashen Afirka zai bai wa kananan manoman Nijeriya tallafin rancen kudi dala miliyan 210 da zimmar habaka ayyukan noma da harkokin kiwo a daukacin fadin Nijeriya.
Wannan shi ne shi ne tallafi na farko karkashin wani shiri na musamman da bankin raya kasashen Afirka ta bullo da shi don rage wa manoma tsadar kaya.
- Muna Ci Gaba Da Kokarin Ceto Sojar Da Aka Sace – SojojiÂ
- Sharhi:Al’ummar Kasar Sin Na Sa Ran Rungumar Sabuwar Rayuwa Cikin Sabuwar Shekara
Har ila yau, shirin zai fara ne da jihohi bakwai, sannan daga baya za a fadada shirin zuwa wasu kasashen Afirka guda bakwai.
A yayin taron zuba jari a kasar Saudiyya a watan Oktoba na shekarar 2021, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce Afirka ce ta fi ko ina yawan kasar yin noma.
Sauran abokan hulda kamar Bankin Raya kasashen Musulunci da kuma Asusun bunkasa noma na kasa da kasa, za su hada hannu wajen tallafa wa aikin.
Hukumar abinci da aikin noma ta Majalisar dinkin duniya ta ce Nijeriya na da yawan gonaki, amma duk da haka kasar na dogaro da shigo da wasu kayan abinci daga waje.