Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da tsige Kwamishinan Addinai na jihar, Dakta Muhammad Tahar Adamu (Baba Impossible) daga mukaminsa.
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labara jihar, Malam Muhammad Garba, ya rabawa manema labarai.
- Sakon Sabuwar Shekara: Na Yi Iya Bakin Kokarina Wajen Yi Wa Nijeriya Hidima A Mulkina — Buhari
- Tsaraba Ga Mata: Hanyoyin Mallakar Miji Cikin Sauki
Sanarwar ta ce gwamnati ta samu Baba Impossible wajen yin gaban kansa na rage ranakun aiki ga ma’aikan ma’aikatarsa ba tare da tuntubar gwamnati ba.
Tun da farko Baba Impossible ya takaita ranakun aiki a ma’aikatar zuwa ranakun Litinin da Talata da Alhamis da kuma Juma’a.
Kazalika, gwamnatin ta ce ta same shi da rashin biyayya ga gwamnati da kuma rashin gudanar da aiki yadda ya kamata.
Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ya aike da sunan Dakta Nazifi Ishaq Bichi na Jami’ar Bayero ga Majalisar Dokokin jihar, domin maye gurbin kwamishinan.
Baba Impossible, shi ne wanda ya jagoranci takaddamar mukabala da wasu malaman jihar suka yi da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da wata kotu a jihae ta yaken wa hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samunsa da laifin batanci ga Fiyayyen Hallita Annabi Muhammad (SAW).