Oleh Podorozhnyy ne ke jagorantar mutane zuwa mutuwarensa mai duhu wadda buhuhunan yashi suka toshe tagoginta.
Da zarar an bude kofofinta na karfe masu nauyi, sai warin gawarwaki ya bigi hancin mutum.
- Ba A Aiwatar Da Wasu Matakai Na Yaki Da COVID-19 Domin Muzgunawa Al’ummar Uygur Ba
- Ba A Aiwatar Da Wasu Matakai Na Yaki Da COVID-19 Domin Muzgunawa Al’ummar Uygur Ba
Kwantenar cike da tudun gawarwakin mutanen da aka kashe lokacin da garin Izyum ke hannun Rasha. Da yawan gawarwakin sun shafe watanni.
Ana yi wa jikkunan lamba da kuma takaitaccen bayani cikin bakin rubutu. Makwanni bayan sake kwato Izyum din, har yanzu ba a tantance sunayen mutum 146 da aka tarar a garin ba.
An kawo su nan ne saboda babbar mutuwaren cike take makil da gawarwarkin da ba a tantance ba da aka kashe sakamakon harin makamai masu linzami na Rasha.
“Adadin mutanen da ba mu tantance ba suna da yawa sosai,” a cewar Oleh, wani mai bincike na cibiyar bincike ta Kharkib Bureau of Forensic Edpertise. “Za su ci gaba da zama a nan yayin da ake kammala gwajin DNA.”
Nema kamar ba za a samu ba
Ana iya ganin barnar da Rasha ta yi a garin Izyum mai yawan gaske. Wani dogon rukunin gidaje ya fuskanci luguden wuta har sai da aka yi wani rami a tsakiya da kuma gefensa, wasu gidajen na gefensa kuma sun zama baraguzai.
Akwai kuma iyalai da ke zaune cikin wannan yanayi kuma suke ci gaba da neman ‘yan uwansu da suka san an kashe su amma ba su ga gawarsu ba.
An lalata ofishin ‘yan sanda na Izyum, saboda haka ‘yan sandan suka kafa wata cibiyar karbar samfurin halittar mutane a wata kwaleji.
Hukumomi na karbar samfurin danshin bakin mutane don gano ‘yan uwansu da aka kashe
Akan kira mutane daya bayan daya kuma a dauki danshin bakinsu. Sai a tura shi ga wata cibiya da za ta ciri kwayar halittar DNA da zimmar gano mai irin wannan samfurin a cikin gawarwakin mutanen.
Baya an dauki nata samfurin, Tetyana Tabakina ta tsaya a tsakiyar dakin da hannunta a baki cikin alhini.
An kashe ‘yar uwarta Iryna, da dan ‘yar uwarta Yebheniy a hare-haren Rasha a gidansu a watan Maris. Yanzu suna zaune a gidan kasa, inda suke ganin ya fi aminci.
Tetyana ta samu damar gane Yebheniy saboda wani zane da ke hannunsa amma har yanzu ba ta iya gano ‘yar uwarta ba.
“Ira ta daidaice a harin. Na kasa ganin komai nata,” in ji ta cikin sanyayyar murya. “Ina jira na samu ko da dan wani abu ne na ‘yar uwata don na binne su tare.”
Wahalhalu game da gwajin DNA
Yakin da ya jefa Tetyana cikin wannan hali shi ne dai ke kara wa neman gawarwakin wahala.
Lokacin da Rasha ta mamaye Kharkib, cikin masu guduwa har da masu binciken gano gawarwaki.
“Muna bai wa wasu horo, amma yanzu mutum takwas kawai gare mu a wannan sashen kuma aikin na nan jibge,” kamar yadda Biktoria Ionoba ya bayyana.
“Akwai kuma matsalar daukewar lantarki. Na’urori masu basira sai su daina aiki nan take, dole sai mun sake komai tun daga farko. Muna da jannareto, amma wani zubin mu kan rasa wuta tsawon rana guda.”
Hanyoyin da wasu ke mutuwa na rikitar da masu bincike: da yawa sun kone sosai a hare-haren.
Bayanan hoto
Hukumomi sun tono gawa kusan 900 a yankin Kharkib Sai dai kuma ba dukkan mamatan ne ke da ‘yan uwan da za su ba da samfuri don gano su ba.
Kaburbura a daji
An binne mafi yawan mutanen da aka kashe a wasu kaburbura a dajin da ke wajen gari.
Masu hakar kabari ‘yan sa-kai ne suka binne su. Lokacin da dakarun Ukraine suka kwato garin a watan Satumba, an tono gawarwakin kuma aka mayar da su Kharkib. ‘Yan sanda sun ce wasu sun mutu ne ta wasu hanyoyi, yayin da aka kashe da yawa a hare-haren Rasha. A yanzu sun tono mutum 899 a fadin yankin.
“Abu ne mai wuya kwarai. Ba mu taba ganin gawarwaki da yawa kamar haka ba. Tsaka-tsaki, muna tono gawar mutum 10 a kullum,” a cewar Serhiy Bolbinob, shugaban sashen bincike na ‘yan sandan Kharkib.
A wannan makon jami’ansa suka gano gawar wani mutum da harin bam ya kashe kuma matarsa ta binne shi a lambun gidansu.
Jimillar gawar mutum 451 aka gano a Izyum, ciki har da yara bakwai.
Bayanan hoto
“Allah ya koya mana yafiya amma ba zan taba yafe wa makasa ba,” in ji Olena Ihnatenko da ta yi jana’izar mijinta
Dogon jira
Zuwa yanzu, gawa biyar kawai aka tantance ta hanyar amfani da DNA a Izyum. Tawagar binciken ta ce wasu daga cikinsu sun lalace sosai suna fargabar ba za a iya gane su ba har abada.
A wajen Tetyana Tabakina, abin ya zama dogon jira.
Ta ce a kwanan nan wani makwabcinta ya binne mutum bakwai dangi daya wadanda aka kashe a harin da ya halaka ‘yar uwarta.
“Ya fada min cewa washegarin ranar da aka binne su kamar an cire masa wani babban nauyi ne kuma sai lokacin ya fara yin barci,” Tetyana ta bayyana.
“Ina so ne kawai na ga bayan lamarin nan, ko abin ya kawo karshe a wajensu cikin sauki ko kuma a wajenmu.”