Tuni dai aka fara karbar katin zabe na dindin a dukkan kananan hukumomin kara nan kamar yadda Hukumar Zabe mai Zaman Kanta (INEC) ta sanar, ta ce, za a fara karbar sabon katin ne a tsakanin ranakun 12 ga watan Disamba zuwa ranar 22 ga watan Janairu na shekarar 2023.
Hukumar ta zartar da cewa, za a cigaba da karbar katin ne a cibiyoyin rajista a mazabu 8,809 na fadin tarayyar kasar nan a tsakanin ranakun da aka zayyana na ranakun 6 zuwa 15 ga watan Janairu shekarar 2023.
- Hada Rubutu Da Karantarwa Ne Babban Kalubalen Da Nake Fuskanta -Amira Sule
- Gwamnatin Kano Ta Tunbuke Kwamishinan Addinai Kan Rashin Mata Biyayya
Rahottanin da suke fitowa daga cibiyoyin kabar ya nuna cewa, Shirin karbar katin yana gamuwa da cikas na abin da ya shafi cunkoso da rudanin rashin tantanace masu karbar katin.
Haka kuma karbar katin a yankin babban birnin tarayyar kasar nan Abuja ya nuna cewa, an karbar katin a lokaci daya a dukkan kananan hukumomi 6 na birnin tarayyar.
A wasu cibiyoyin karbar katin a yankin Abuja, al’umma da suka yi rajista na taruruwan sun sun fito domin karbar katin amma babu isassun ma’aikatan da za su saurare su tare da basu katin zaben, cunkoson ya haifar da babbar matsala a wasu cibiyon kabar katin.
Haka kuma an samu bayanan cewa, an cigaba da bayar da katin a wasu mazabu, duk da cewa hakan ya danganta ne da yadda mutum ya yi rajistar tunda farko yin rajistar, ko mutum ya tashi ne daga wani gari zuwa wani ko kumu yana neman a sake masa katin a dalilin bacewa ko salwanta, ko kuma wasu dalilai na daban.
Kamar yadda aka yi tunani al’umma da dama da suka tattauna da manema labari sun nuna damuwarsu a kan yadda shirin rarraba katin ke gudana, wasu na yabawa wasu kuma na nuna damuwarsu a kan yadda ake bayar da katin. A yayin da wasu da aka tattauana da su suka jinjina tare da yabawa da yadda jami’an hukumar INEC suke tafiyar da shirin raba katin sai dai sun yi korafin yadda ba a yi cikakken tsarin ba, abin da ya kai ga wahalar da mutane da dama da suka nufi cibiyoyin karbar katin zabensu na dindindin.
A mastayinmu na dan jarida mun yi imanin cewa, bai kamata a ce, karbar katin zaben ya zama wani abin da za a sha wahala a kai ba. Tunda akwai sauran lokaci da aka ayyana na karbar katin ya kamata a ce, INEC ta kara kaimin yadda take gudanar da shirin.
Muna sane da yadda hukumar ke fama matsalolin gurbatattun ‘yan siyasa da ke kokarin kawo cikas ga tsarin shirin gudanar da zaben gaba daya don cimma burin kashin kansu. Tabbas ina sane cewa, INEC na fuskantar manyan matsaloli a halin yanzu.
Amma kuma in aka lura da yadda aka fuskanci rudai a lokacin da aka yi rajistar yakamata a ace an dauki darussa ta yadda karbar katin a wanna lokacin ya zama a cikin sauki ga masu karbar katin a sassan Nijeriya. Tun da aka fara fuskantar wadannan matsalolin yakamata a ce, INEC ta dauiki matakin sake fasalin yadda ake rarraba katin duk shi dan Nijeriya gwamnace ya yi komai a lokacin da al’amurra suka kure.
Ana iya ganin wannan a lokacin da aka yi rajistar katin inda sai daga karshe mutane suka yi ta tururwa don katin abin da sanya har sai da aka ta kiraye-kirayen neman a kara wa’adin cigaba da bayar da katin, magana har sai da ta kai ga hukuncin kotu na nemi a kara wa’adin lokacin yin rajistar.
A kan haka yakamata ace. Hukumar ta samar ya yanayin da karbar ya zo a cikin sai tun a karon farko don a kulle bakin masu kokarfi wadanda basu ganin alhairi a dukkan ayyukan da hukumar take yi a dukkan lokaci.
Kamar dai yadda ta yi a lokacin da ake yi wa al’umma rajistar kantin zaben, yakamata a INEC ta samar da cibiyoyin karbar katin zabe a kusa da al’umma tare da kuma fadakar da mutane bukatar fitowarsu don karbar katin zaben domin kuwa in har mutum bashi da katin zaben bashi ba zabe a 2023.
Dokar zabe ta shekara 2023 ta tanadi cewa, dole sai in mutum yana da katin zabe ne akwai zai samu damar kada kuri’a a kan dole ta samar da yanayin da kowa zai samu karbar katin zaben don ya sauke nauyin da ke kansa na zaban wanda yake so ya mulke shi a shekarar 2023.
Ya kuma kamata jam’iyyun siyasa su kara kaimi wajen fadakar da mambobin su a kan bukatar fitowa don su karbi katin zaben ba wai kawai su bar wa gwamnati aikin fadakawar ba. A daidai lokacin da muke da kasa da kwanaki 50 zuwa ranar da za a gudanar da zaben, lallai babu wani lokaci da za a bata.