A ranar Talatar data gabata ne dai aka binne gawar shahararren dan wasan kwallon kafar nan na duniya, Pele, wanda ya mutu a ranar Alhamis ta satin da ya gabata yana da shekara 82 a duniya.
Dubban masu makoki ne suka hallara a filin wasan Santos na Brazil, domin ganawa da gawar tsohon dan wasan duniyar kuma an ajiye gawar Pele a tsakiyar filin Urbano Caldiera da ke Sao Paulo, yayin da magoya baya suka yi dogon layi suna tozali da ita.
Tsohon dan wasan wanda ya kafa tarihin cin kofin duniya sau uku a tarihi, ya mutu ne bayan ya sha fama da jinya wadda ya dade yanayi kuma a wasu lokuta a baya ma aka dinga yada jita-jitar cewa ya mutu.
Daga cikin manyan bakin da suka halarci jana’izar akwai shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Gianni Infantino, wanda ya ce za su bukaci kowace kasa a duniya ta saka sunan Pele a daya daga cikin filayenta.
Kasancewar Pele daya daga cikin manyan taurarin matasan bakaken fata a fagen wasanni a zamanin talabijin, Pelé ya samu karbuwa da kauna daga ‘yan Afirka a fadin nahiyar gaba daya.
A lokacin da kasashen Afirka ke fafutukar samun ‘yancin- kai a karshe-karshen shekarun 1950 da kuma farko-farkon shekarar 1960, Pelé ya dinga samun gayyata daga kasashen Afirka da suka samu ‘yanci, domin wasan sada zumunta da kungiyar sa ta Santos FC da kuma tawagar kasar sa ta Brazil.
A tarihin sa da ya rubuta, Pelé ya bayyana cewa wadannan tafiye-tafiye da ya yi zuwa kasashen Afirka a wannan lokaci ba kawai sun sauya yadda yake kallon duniya ba har ma da yadda ya ce duniya ta dauke shi.
Mutumin da ya rubuta kundin kungiyar kwallon kafa ta Santos, Guilherme Nascimento, ya yi daidai kamar yadda ya nuna cewa wadannan tafiye-tafiye zuwa Afirka na cike da labarai wadanda kusan da wuya a iya bambancewa tsakanin na gaskiya da kuma na kunne-ya-girmi-kaka.
A misali, zuwan Pelé Algeria, ya kasance kamar wani abu na fim. A shekarar 1965, tauraron wanda a lokacin yana da shekara 24 ya je kasar a daidai lokacin da darektan fim, Gillo Pontecorbo yake hada fim din ”The Battle of Algiers”.
A kan haka sai abin ya zo daidai da lokacin da za ka ga tankokin yaki suna ta kai-komo a fadin kasar kama daga kauyuka zuwa Casbah sannan shugaban kasar na wancan lokaci Ahmed Ben Bella, mai matukar sha’awar wasan kwallon kafa ya shirya wasan sada zumunta biyu domin wannan ziyara.
Sai dai kuma ministan tsaro na lokacin Houari Boumediene ya yi juiyin mulki inda ya hambarar da Shugaba Ben Bella, saboda haka ya soke daya wasan sada zumuntar wasu ‘yan jarida da masu fashin baki sun ce ministan ya yi amfani da yanayin da ake ciki na ruguguguwa da murnar zuwan tauraron kwalon kafar, a matsayin wata hanya ta dauke hankali ya yi juyin mulkin.
Sai dai tarin ziyarar da Pele ya dinga kaiwa Moroko a matsayin sa na tauraron kwallon kafa a lokacin ba su kai kamar na wasu ba sannan an ce ya yi wasu kalamai masu dadadawa da yabo ga tawagar kasar da ta je gasar cin Kofin Duniya a 1970 a Medico, kasancewar ita ce kasa ta farko a Afirka da ta fara samun gurbin wannan gasa ta duniya tun bayan Masar a 1934.
A lokacin wata ziyarar kuma an ce Pele ya yi magana a kan tauraron kwallon kafar kasar ta Moroko na zamanin wato Larbi Ben Barek, wanda ya buga wasa a kungiyoyin Olympikue de Marseille da Atletico Madrid.
Ziyarar Pele zuwa Najeriya da kuma Jamhuriyar Dumukuradiyyar Kongo ita ma ta kasance cike da labarai iri-iri ko dai na gaskiya ko kuma na kanzon-kurege a lokacin zuwansa kasashen biyu an ce ya sa an samu dakatar da bude wuta a kasashen masu karcar bakuncinsa yakin basasa da suke yi.
An yi yakin basasar Najeriya daga shekarar 1967 zuwa 1970, amma duk da haka ana cewa lokacin da ya je domin wani wasa na karramawa da tawagar kwllon Najeriya, an dakatar da bude wuta a yakin tsawon sa’a 48.
Sai dai Pelen da kansa a littafin sa ya rubuta cewa, ba shi da tabbacin cewa lalle gaskiya ne amma ya kara da cewa ‘yan Najeriyar lalle sun dauki matakan tabbatar da cewa ‘yan Biyafara ba su mamayi Lagos ba a lokacin da suke can, yana mai tuna irin tarin sojojin da aka baza a birnin.
Ana wannan magana ce kuwa duk da cewa fa ba ta yadda ‘yan awaren na Biyafara za su iya yin hakan domin suna nisan akalla kilomita 500 ne tsakaninsu da Lagos, hasali ma sojojin Najeriya suna tura su baya a lokacin.
A shekarar 1976, kamfanin lemon kwalba na Amurka, Pepsi ya yi amfani da farin jinin Pele a nahiyar Afirka wajen tallata lemon, inda ya dauki nauyin ziyarar tauraron zuwa Afirka ta Gabas, a kasashen Kenya da Uganda.
A lokacin Sarkin kwallon kamar yadda ake masa lakabi ya yi nasarar tallata lemon tare da gudanar da wasu sansanoni na matasan ‘yan wasa a kasashen biyu. Sannan a Kenya ‘yan kallo sun bayar da murfin kwalbar lemon kafin su shiga kallo, inda manya suke bayar da shida yara kuma uku.
A duk tsawon wadannan shekaru, Pelé ya kuma ziyarci kasashen Mozambikue da Masar da Sudan da Senegal da kuma Ghana sannan bayan ziyarce-ziyarcen masu tarihi, Pelé ya kasance wata alama ta karfafa guiwa da zama abin koyi ga ‘yan kwallon kafa masu tasowa a nan nahiyar Afirka.
Darajar Pele a duniya ce tasa daya daga cikin fitattu kuma manyan gwarazan ‘yan kwallon kafa na Ghana, ya lakaba suna Pele a cikin sunan sa inda ake kiransa da Abedi “Pele” Ayew inda ya ce daukakarsa ta karfafa masa guiwa, wanda hakan ya sa ya dauki sunasan Pele ya yi lakabi da shi domin ya zama kamar sa a tsawon rayuwarsa ta kwallon kafa, har ma bayanta, wanda wannan ba karamar daraja ba ce.
Har kullum Pelé ya kasance mai kyakkyawan fata da kishin ci-gaban Afirka a gasar Kofin Duniya kuma hasashen da ya yi a tsakiyar shekarun 1970 cewa wata kasar Afirka za ta ci Kofin Duniya kafin shekara ta 2000, ya kasance abin tattauna wa sosai kafin fara duk wata gasa ta Kofin Duniya tun daga lokacin da ya yi furucin.
Saboda haka abu ne da ya yi daidai kasancewar sakonninsa na karshe a shafukan internet sun hada da na taya murna da ya yi ga kasar Moroko kan rawar da ta taka ta a-zo-a-gani wadda ta kasance tarihi a gasar Kofin Duniy da aka yi a Katar.
A jawabin sa a shafinsa na twitter akan tawagar kasar Moroko, Pele ya ce “Ba zan kasa taya Moroko murna ba a kan gagarumin kokarin da suka yi kuma abin alfahari ne a ga Afirka ta yi fice.” Kamar yadda ya rubuta a sakon.