Wani jigo a jam’iyyar APC a karamar hukumar Zariya, Alhaji Aliyu Sa’idu ya bayyana cewa ayyukan ci gaba da gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed el-rufa’i ya gudanar musamman a kananan hukumomin Sabon Gari da Zariya zai bar tarihin da za a dade ana tunawa da shi shekaru masu yawan gaske a daukacin Jihar Kaduna baki daya.
Wani jigo a jam’iyyar APC ya yi wannan yabo ne a lokacin da yake yin tsokaci kan ayyukan ci gaban al’umma da Gwamna el-rufa’i ya aiwatar wa al’ummar Jihar Kaduna za su dade suna morawa.
Alhaji Aliyu ya ci gaba da cewa shekaru da yawan gaske da suka gabata, al’ummar Jihar Kaduna ke bukatar wadannan ayyuka daga gwamnatocin da suka shude.
A cewarsa, gwamnonin da suka gabata sun kasa gudanar da ayyuka irin wadannan sai dai tudin alkawarin da suke yi wa al’umma har suka bar mulkin ba su cika ba.
Ya bayar da misali da sabbin hanyoyin da gwamnatin Jihar Kaduna ta yi su a birnin Zariya da suka hada da wadda ta tashi daga kasuwar birnin Zariya zuwa Kofar Galadima da wadda ta tashi daga Kwanar Matasa a Unguwar Lalli zuwa Kofar Doka da wadda ta tashi daga Kofar Jatau zuwa Ofishin ‘yan sanda na birnin Zariya.
Ya ce sauran ayyukan hanyoyi da gwamnatin Jihar Kaduna ta yi a karamar hukumar Sabon Garin Zariya musamman a Unguwar Turawa (GRA) suna da yawan gaske, da duk wanda ya san wadannan hanyoyi kafin el-Rufa’i ya zama gwamnan Jihar Kaduna, ya san cewa an yi abin da ya kamata.