Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya jajanta wa gwamnati da al’ummar Jihar Kebbi kan asarar rayuka, biyo bayan kifewar wani jirgin ruwa da ke jigilar manoma jihar.
A cikin sakon ta’aziyyar da mai magana da yawunsa, Mista Femi Adesina, ya fitar a ranar Juma’a a Abuja, Buhari ya jajanta wa iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu a hatsarin.
- Ba Abin Da Zai Hana Tinubu Lashe Zaben Shugaban Kasa – Gwamnan Kwara
- Sin Ta Yi Imani Da Karfin Jama’Ar Habasha Na Magance Harkokinsu Da Kansu
Ya kuma bukaci a yi addu’o’i ga wadanda aka ceto da har yanzu ake duba lafiyarsu da kuma kula da su.
Buhari ya yaba da kokarin ma’aikatan ceto da suka yi kwanaki suna neman mutanen da suka bace.
Sai dai ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su mai da hankali kan yadda ya kamata wajen tafiyar da jiragen ruwa musamman a yankunan karkara.
Shugaba Buhari ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu.