Tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ce goyon baya da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, LP da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya yi, babban kuskure ne.
Lamido, wanda ya kasance Ministan Harkokin Waje a zamanin gwamnatin Obasanjo, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Bamaina, mahaifarsa, kusa da karamar hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa.
- Ba Abin Da Zai Hana Tinubu Lashe Zaben Shugaban Kasa – Gwamnan Kwara
- “Sabon Ci Gaban Kasar Sin, Da Sabbin Damammaki Na Duniya” An Gudanar Da Zagayen Tattaunawa Na Turai-Asiya A Nan Birnin Beijing
“Obasanjo shugabana ne, na yi yarda da shi, amma kuma mutum ne, yana iya yin kuskure. Don haka ya yi kuskure.
“Babban kuskure ne a gare shi ya amince da dan takarar da ba na jam’iyyarsa ba, wanda ya ba shi nagarta, muhimmanci, martaba a duniya don zama shugaba.
“Ba za ku yi haka ba saboda matasa masu tasowa.
Tsohon gwamnan ya ce mutane sun kasa fahimtar cewa idan jam’iyya ta karrama su, ya kamata su mutunta jam’iyyar.
“Don haka Obasanjo yana magana ne saboda tsohon shugaban Nijeriya ne, idan ba haka mai zai kai shi yin magana haka. Duk abin da yake cewa yanzu saboda shi tsohon shugaban Nijeriya ne daga PDP.
“Don haka PDP ce ta samar da shi kuma ta karrama shi. Don haka ya kamata shugaba ya zama mai bi a sannu, mai zaburarwa, kuma ya kamata ya iya yi wa Nijeriya sabuwar hanya ta yadda mabiyansa za su ci gaba daga inda ta tsaya” in ji shi.