Jami’an hukumar kula da shige da fice (NIS) na jihar Bayelsa, da ke bincike a tolget na Yenagoa sun ceto wani karamin yaro dan kasar waje mai kimanin shekara 12, da ya bace yana gararamba.
An samu yaron yana duba inda zai je a kusa da inda ake binciken ababen hawa, sai aka kawo shi wurin jami’an hukumar kula da shige da fice wanda suka samu nasarar gano inda dangin kabilarsa suke.
Shi dai wannan yaron mai suna Tobi Fred, ya fito ne daga yankin Banigbe-Lokossa da ke Kwatano babban birnin jamhuriyar Benin.
Binciken da aka yi ya nuna cewa, yaron ba ya fahimtar harshen Ingilishi, sai dai yaren Beninoise, sai da mataimakin shugaban al’ummar Beninoise da ke Bayelsa, Mista Etienne Fred, wanda aka ce dan uwan baban yaron ne yanzu haka ba ya kauyen, ba kuma a ji labarinsa ba har lokacin hada wannan labarin.
Yanzu haka dai yaron na karkashin kulawar NIS, ta jihar Bayelsa wanda kuma likitoci ke ci gaba da kula wa da shi, kafin a mika shi ga al’ummar Beninoise domin su mika shi ga iyayensa da ke Banigbe-Lokossa, a Kwatano da ke jamhuriyar Benin.
Haka kuma saboda gabatowar zaben 2023, NIS ta kara tsaurara tsaro kan wadanda ba ‘yan Nijeriya ba, suke zirga-zirga a jihar ta Yenagoa ba tare da izini ba,tun daga lokacin da hukumar ta kaddamar da shirin sa ido na musamman a cikin watan Satumba na,2022, har yanzu hukumar ba ta yi sako-sako da bakin hauren da ke zaune cikin kasa ba tare da izini ba.