Hukumar kula da shige da fice reshen jihar Bayelsa karkashin jagorancin Kwanturola James Sunday, ta ƙaddamar da ƙawata muhallinta da dashen itatuwa.
Hukumar wacce ta dasa itatuwa 30 tun daga mashigar shalkwatar hukumar da ke Bayelsa domin kare muhallinta daga kwararowar hamada da taimaka wa muhalli tare da kawata ofishin ta hanyar shuke-shuken da suka dace.
A wata sanarwar da Jami’in watsa labarai na hukumar NIS reshen Bayelsa ya fitar, ya kara da cewa, za a ci gaba da gudanar da aikin dashen itatuwar a tsohon ofishin hukumar da yanzu aka maida shi barikin Immigration da ke Yenagoa, ofishin yin aikin Fasfo dukkanin da suke cikin garin na Yenagoa.
Sanarwar ta ce, kyautata muhalli na daga cikin abun da ke zuciyar hukumar, kuma za su cigaba da yin kokarinsu wajen kyautata muhallai, ya kuma ce, za su cigaba da yin aikin hadin guiwa da sauran kungiyoyin da abun ya shafa domin inganta tsaron muhalli da kyautata shi.
A gefe guda ya sanar da cewa, hukumar ta dukufa wajen yin ayyukan hidimta wa jama’an kasa da ma na kasashen waje ta hanyar gudanar da ayyuka masu inganci da nagarta.
Hukumar ta yi amfani da wannan damar wajen kira ga jama’an gari da cewa duk wani da ke da wata korafi kan wani jami’in hukumar da ya saba ka’idar aikin da ke gabansa to ya garzaya ya shigar da korafi ga ofishin kwanturula da ke Bayelsa domin daukan matakin dalabtarwa.
Ya ce, NIS ba za ta lamunci kauce wa ka’idar aiki da musguna wa jama’a daga wajen kowani jami’insu ba, don haka ne ya ce akwai matakin hukunci ga duk wanda aka samu da laifi.