A yau Litinin 16 ga watan Janairun nan ne, mataimakin ministan wajen kasar Sin Xie Feng, ya gabatar da jawabin bude taron bana, na dandalin nazarin manyan fannonin raya tattalin arziki, da taron dandalin kwararru na 4, game da tasirin Sin a harkokin kasa da kasa.
Cikin jawabin na sa, Xie Feng ya ce Sin a shirye take ta bunkasa matakan kara bude kofa, da samar da damammakin zurfafa hadin gwiwar cimma moriyar juna.
Xie Feng ya ce a baya bayan nan, Sin ta inganta, tare da sauya matakan ta na kandagarki da shawo kan annobar COVID-19 bisa yanayin da kasar ke ciki, tare da kara bude kofofin kasar ga duniya, matakin da ba ya ga share fage da ya yi na daidaita, da farfado da fannonin tattalin arzikin kasar Sin, matakin ya kuma ingiza sabon karsashi ga farfadowar tattalin arzikin duniya baki daya, matakin da ya samu matukar karbuwa tsakanin sassan kasa da kasa.
Xie Feng ya kara da cewa, Sin na dora muhimmancin gaske, kan wadannan bayanai, tana kuma fatan Amurka za ta dauki matakai na aiwatar da su yadda ya kamata. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan daga CMG Hausa)