Akalla mutane 18 ne suka mutu yayin da wasu 40 suka jikkata a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a karamar hukumar Illela a Jihar Sokoto.
Hatsarin ya rutsa da wata motar haya da kuma motar daukar shanu.
- Akwai Hatsarin Gaske Mika Mulkin Nijeriya A Hannun Tinubu ko Obi – Atiku
- Yadda Ake Gyaran Gashi Na Musamman
Kakakin rundunar ’yansandan Jihar Kebbi, Nafiu Abubakar, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a yammacin ranar Litinin, ya ce lamarin ya faru ne a mahadar Malisa da ke karamar Hukumar Gwandu a jihar.
Ya bayyana cewa hatsarin da ya faru a ranar Lahadin da ta gabata wanda ya shafi direban wata babbar mota mai lamba SRP 442 XA, Jihar Neja da kuma wata mota wadda ta yi jigilar fasinjoji da shanu daga Unguwar Illela zuwa Legas.
Daga nan sai motar ta fadi mahadar Malisa, lamarin da ya yi sanadin mutuwar shanu 16.
Ya kara da cewa kwamishinan ‘yansandan jihar, Ahmed Kontagora ya ziyarci inda hatsarin ya afku, inda ya shaida yadda aka kwashe mutanen zuwa babban asibitin Gwandu inda daraktan kiwon lafiya na asibitin ya tabbatar da mutuwar mutane 18.
Bugu da kari, ya ce wadanda suka jikkata suna karbar magani a asibiti.
Kwamishinan, ya yi kira ga masu amfani da ababen hawa da suke bi matakan hanya kuma su kasance masu hankali yayin tuki.
Ya kuma shawarci direbobi da su rika kiyaye ka’idojin tuki sannan su guji yin lodin da ya wuce kima.
CP Kontagora ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu ya kuma jikansu da rahama.