Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta kama wani Tasi’u Abdu da ke garin Hayin Fago a karamar hukumar Dawakin Tofa, dauke da kati nan zabe.
Kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa ne, ya tabbatar wa da jaridar LEADERSHIP labarin da yammacin ranar Alhamis.
- Na Sake Dawowa Musulunci, Cewar JJC Skills
- Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Ci Gaba A Sabon Zamani Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba
Kiyawa ya ce jami’an rundunar na ci gaba da bincike a kan lamarin.
Wata majiya ta bayyana cewa wanda ake zargin yana da alaka da dan takarar majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Tofa da Dawakin Tofa da Rimin Gado a jam’iyyar APC, Abba Umar Ganduje
A kwanakin baya ma sai da rundunar ta kama wani dauke da katin zabe wanda tuni aka gurfanar da shi a gaban kotu.
A ranar 25 ga watan Fabrairu ne dai za a yi zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya da na dattijai.