Elizabeth Homes, sunanta ya karade mujallu da jaridu da shafukan intenet a kasashen duniya saboda sa’arta da fikirar da Allah ya bata wajen yin kasuwnacin zamani ta hanyar kimiyya da fasaha. Elizabeth Homes ana kwatanta ta fasaharta da marigayi Stebe Jobs mai kamfanin Apple wato masu samar da wayoyin Iphone da sauransu.
Shekaru biyar a baya Elizabeth Homes ta mallaki kudi Dalar Amurka biliyan hudu a sanadiyyar katafaren kamfanin da ta kafa mai suna Theranos a Amurka. Sannan akalla an yi wa shi wannan kamfani nata kima inda ya kai Dalar Amurka biliyan 10.
- Tabarbarewar Aikin Gwamnati A Matakin Jihohi
- Kuskuren Shugabannin Baya Ne Ya Jefa Nijeriya Cikin Tsaka Mai Wuya – Kwankwaso
Yadda ta fara kasuwancinta?
Elizabeth Homes kamar yadda wani shahararren dan jarida mai binciken kwakwaf kuma marubuci ya wallafa a wani sabon littafinsa da ya rubuta akan Elizabeth Homes, Mista John Carriyou ya ce, tun farko dalibar Jami’ar Stanford ce amma saboda wasu dalilai aka kore ta daga jami’ar ta yadda ta fara sama wa kanta mafita, inda ta fara had-hadar kasuwanci ta bangaren kimiyya da fasaha a shahararren wajen nan na kamfanoni masu tasowa a Amurka wato Silicon Balley.
Elizabeth ta hadu da wani mutum dan asalin Indiya mai suna Ramesh Balwani a inda suka fara soyayya kuma ta zama farkarsa, ko da yake ta fada wa kotu daga karshe cewa Balwani ya yi amfani da shakuwarsu tare ya ci mutuncinta. Ita da Balwani sun fara tunanin kirkirar wata fasaha wacce za ta zama a duniya babu irinta ta bangaren kiwon lafiya.
Wannan wace fasaha ce?
Fasahar ita ce za su kirkiri wani abu wanda zai rinka yi wa mutane gwajin jini amma abin mamakin wannan fasaha ita ce sau daya tak za’a soki mutum a dauki jininsa a inda a cikin ‘yan dakiku kadan zai fadi duk abin da mutum ya ke fama da shi a jikinsa. Hakika wannan fasaha ta motsa mutane ta yadda kowa ya ji ya gamsu inda kuma ta sa mutane za su yarda cewa yanzu ba sai mutum ya je ana yi masa gwaje-gwaje ba akan rashin lafiya ba, wannan abin kadai ya isa kowa ya san menene abin da ya ke damunsa.
Sun kirkiri wannan fasaha wacce suka sa mata suna Edison. Wato Edison wata na’ura ce ‘yar karama kamar kafso na magani yadda za ta dauki jini sannan ta bayar da sakamako nan take. Sannan kirkirar wannan fasaha ta sa masu zuba jari, sun zuba wa kamfanin Theranos Dala biliyan daya saboda yadda wannan kamfani ya yi bayanin ita wannan fasaha.
Manyan mutane a Amurka kamar Tsohon Sakataren Harkokin Cikin Gida Dattijo Henry Kessinger da wasu faitattun sanatocin Amurka inda suka zama mambobin gudanarwa na kamfanin Theranos. Kuma duk sun yi haka ne saboda yadda wannan kamfani ya gabatar da wannan sabuwar fasahar ta yadda a tunaninsu zai canja al’amuran kiwon lafiya a duniya.
Kamfanin Theranos ya zama wani kamfani wanda ya nuna alamar fara gogayya ta fannin kere-kere da fasaha da kamfanin Apple masu Iphone.
Daga shekarar 2014 wannan na’ura wato Edison ta shiga kasuwa inda mutane suka fara amfani da ita wajen gwaje-gwajen lafiyarsu. Amma kash tun kafin a je ko ina ita wannan fasaha ta fara bayar da wasu bayanai wadanda masu amfani da ita suka fara shakku akan ingancinta. Wannan ce ta sa shi Mista John Carriyou ya fara tunanin fara binkicen kwakwaf kan wannan katafaren kamfani na Theranos.
Kafin nan, abin da har ila yau ya fara shiga zukatan Amerikawa shi ne yada Elizabeth ita da saurayinta suke rayuwa cikin alatu mai cike da kashe kudi. Gidan da suke zaune an yi masa kiyasin ya kai Dalar Amurka miliyan 15, sannan duk inda za su je suna shiga jirgin kasaita na musamman wanda suka saya. Sannan a lokacin Shugaba Donald Trump har White House suke zuwa don cin abinci da shugaban kasa, ko da yake wani mai bincike shima ya ce wata kil Donald Trump ma ya zuba na sa kason don samun riba.
A 2016 abubuwa sun fara yawa wato ma’ana mutane sai kuma korafi suke yi akan wannan fasaha ta Edison. Kamar yadda na fada a baya Carriyou ya fara binciken sirri a wannan kamfani tun daga 2015 a inda ya rinka bibiyar ma’aikatan kamfanin na Theranos musamman wadanda kamfanin ya sallama daga aiki. Sannan Carriyou ya samu wani a cikin kamfanin wanda kakansa ne Henry Kessinger yana da jari a kamfanin inda ya rinka bashi bayanan sirri sosai a kan kamfanin da abinda suke samarwa.
Kafin Carryou ya juyar da binkicensa ya koma littafi, bayan abubuwan da ya samo a lokacin yana binciken kamfanin ya zakulo yadda Elizabeth ta rinka tsoratar da duk wani ma’aikaci a kamfanin da ya nuna shakku akan abin da suke yi. Saboda abin da ya faru da yawa ma’aikatan kamfanin sun gano cewa wannan aikin da Edison ya kamata ya yi na gano abin da yake damun jama’a ba ya yi.