Gwamnatin Jihar Bauchi ta bukaci al’ummomin Musulmi da Kiristoci mazauna unguwannin Yolan Bayara da ke cikin gundumar Miri da ke Bauchi da su kai zukatunsu nesa don samar da zaman lafiya tare da cewa har yanzu filin Makabarta da ake kokarin tada jijiyar wuya a kai har yanzu gwamnatin jihar ba ta bai wa kowa ko wata kungiyar ba.
LEADERSHIP HAUSA ta labarto cewa, rashin fahimtar ya samu asali ne sakamakon furucin da shugaban CAN a jihar Bauchi Rabaran Abraham Demius Damin ya yi na cewa gwamnatin jihar ta ba su fili mai girman kadada 50 domin su gina makabarta.
- Musulmai Sun Fusata Da Matakin Gwamnatin Bauchi Kan Makabarta
- Rikicin Warware Rawanin Tsohon Wazirin Bauchi Na Ci Gaba Da Daukar Sabon Salo
Da ya ke ganawa da ‘yan jarida kan lamarin, Babban hadimin gwamnan Jihar kan hulda da ‘yan jarida da yada labarai, Kwamared Mukhtar Gidado, ya tabbatar da cewa, filin makabarta da aka takaddama akan sa, har ya zuwa wannan lokaci ba a bayar da shi wa wani ko kungiya ba.
Gidado wanda ke yana mayar da martani ne bisa koke da al’ummar Musulmi mazauna Yolan-Bayara suka yi a kwanakin baya dangane da wannan lamari, yana mai cewar, gwamnati takan bayar da filin kasa ne bisa bukatar da ta shafi al’umma.
Ya ce, “Abin da ke faruwa shi ne, Kungiyar Mabiya Addninin Kiristanci (CAN) ta rubuta wa gwamnati takarda tare da bukatar a ba su wani fili da za su mayar da shi makabartar mabiya addinin su a nan yankin Bayara dake cikin garin Bauchi.
“Gwamnatin jiha ta bayar da umarnin a duba wani fili a farfajiyar wadannan al’ummai mai kimanin kadada hamsin (50) bisa dubi da cancantar a bai wa masu wadannan bukata bayan bibiyar dukkan ka’idoji na doka da suka dace da yin hakan, daga cikin babban filin da yake da murabba’in kadada 470 dake cikin wannan yanki na mazaunar wadannan al’ummai.
“Dangane da nazarce-nazarce da suka jibanci bayar da wannan fili da ake bukata, ya sa gwamnatin jiha ta kafa wani kwamiti a karkashin jagorancin mataimakin Gwamna, Sanata Baba Salihu Tela, hadi da wasu kwararru akan lamuran yin amfani da fili da safiyon sa, wadanda za su yi nazarin bayar da filin ga mabukata”.
Ya kwamitin da aka kafa zai yi nazarin duba wannan fili da ake bukata, tare da shawartar gwamnati bisa yin abin da ya dace, yana mai cewa, “Sai kwatsam al’ummar Musulmi na wannan gunduma suka rubuta wa gwamnati takardar koke da nunin cewa wannan fili na tasu al’umma ce”.
“Wannan fili da ake yin husuma akan sa, har zuwa wannan lokaci ba a bayar da shi wa kowa ba, domin har yanzu gwamnati tana cikin yin nazarin duba ka’idojin bayar da shi, kuma wajibi ne jama’a su san cewa a duk wani yanayi da gwamnati za ta bayar da filin kasa, walau wa daidaikun jama’a ne ko kungiyoyi, takan yi dubi da ka’idoji ne kamar yadda dokar fili ta zayyana, tare da yin nazarin diyya daya kamata a bai wa masu mallakar filin idan ya kasance na daidaikun jama’a ne ko al’umma”.
Mai bayar da shawara wa gwamna ya bayyana cewar, dukkan al’umman guda biyu, Musulmi da Kiristoci su na da ‘yancin neman fili daga wajen gwamnati domin bukatar samar da makabarta, sai sai ya ce sai an bi komai bisa ka’ida kafin.
Su dai al’ummar musulmi mazauna Yolan-Bayara sun gudana da wani taron manema labarai, inda suka nuna rashin gamsuwarsu bisa filin makabarta da suke kyautata zaton an bai wa al’ummar mabiya addinin kiristanci, su na masu cewar, wannan fili da aka bayar na kakanin-kakanin su ne.
Tawagar ta al’ummar Musulmi na Yolan Bayara ta gudanar da taron manema labaran ne a karkashin jagorancin Sani Sarki Yakubu wanda ya bayyana cewar, filin da suke yin magana akai na iyaye da kakanin su ne wanda a tuntuni ya kasance makabarta ce ta al’ummar Musulmi, wanda har ya zuwa wannan lokaci suke bunne mamatan su, don haka idan ya sake kasance wa makabartar mabiya addinin kiristanci, zai kasance ana tone mamatan Musulmi, ana musanyawa da mamatan ma’abutan wani addini, su na ganin yin hakan ba zai dadada wa kowane jinsin addini ba.
Yakubu ya ce ko kadan ba su adawa da bai wa kiristoci fili don su yi makabarta amma dai bai kamata a mallakar musu filin da tunin aka fara bisne musulmai a ciki ba.
“Su Kiristoci, ‘yan-wan mu ne maza da mata, kuma tare muke zaune shekaru aru-aru cikin kwanciyar hankali da lumana a tsakanin mu, don haka bamu kaunar wani sabani a tsakanin mu. Kuma mu masu biyayya ne wa gwamnati, kuma masu bin doka”, in ji jagora Sani Yakubu.