Hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS) reshen jihar Bayelsa a karkashin jagorancin Kwanturola James Sunday, ta fara horas da manyan jami’anta kan tsari da inganta aiki yayin da kuma ake horas da kananan jami’ai kan yadda za su kware wajen saffara makamai a Yenagoa da ke jihar.
Horaswar wacce ta kasance na kwana guda ga manyan jami’an yayin da su kuma kananan jami’an da ake horas da su kan saffara makamai za su shafe tsawon mako guda su na amsar horon.
Da ya ke tofa albarkacin bakinsa kan wannan horaswar, Kwanturola James Sunday, ya ce an dauki wannan matakin ne domin yadda za a kara wa manyan jami’an ilimin yadda za su gudanar da aiki a yayin babban zaben 2023 cikin kwanciyar hankali da kwarewa.
Ya ce, “Haramun ne wani jami’i ya tsunduma cikin siyasa, aikinmu a fayyayace yake a kan zabe shi ne yi aikin wucin gadi ko na musamman domin tabbatar da komai sun tafi daidai. Tare da hadin guiwa da sauran takwarorinmu na tsaro, za mu bayar da gudunmawa wajen tabbatar da zaben ya gudana cikin inganci da sahihanci. Don haka wannan horaswar ta za taimaka sosai wa kowani jami’i ya samu gogewar yadda zai tafiyar da aikinsa a kowani lokaci.”
A sanarwar da Kakakin hukumar NIS reshen jihar Bayelsa ya fitar tare da aiko da kwafinta wa LEADERSHIP Hausa, ya kara da cewa, “Ba za mu yi sako-sako da kyautata tsaro a yayin zaben da ke tafe ba, babban aikin da ke gabanmu shi ne mu tabbatar cewa babu wani dan wata kasa (da ba Nijeriya ba) da ya shiga ko tsoma kansa cikin harkokin zaben Nijeriya. Kan hakan an jawo hankalin jami’anmu da su kara kwazo waje kula da masu shige da masu fice domin tabbatar da tsaro a dukkanin iyakokin shige da fice.
“Kuma a tabbatar an cafke wani dan wata kasa da ya yi kokarin kutse cikin harkokin zaben kasar nan.”
Ya gargadi jami’ansu da su tabbatar sun tafiyar da komai bisa kwarewa da bin dokokin aiki a kowani lokacin.
Dangane da masu samun horo kan makamai kuwa, an shawarce da su maida hankali domin cimma manufar da ake ba su horon a kai na ganin sun samu cikakken kwarewar yadda za su tafiyar da makaman da su hannunsu a yayin da suke bakunan aikinsu.