Wasu ‘yan bindiga sun kashe kwamandan tsaron Ebubeagu na gundumar Ogboji da ke karamar hukumar Ezza ta Arewa a Jihar Ebonyi.
LEADERSHIP ta tattaro cewa, ‘yan bindigan sun mamaye gidansa da ke yankin Ogboji wajajen karfe 1 na safiya tare da kasheshi gami da yin gaba da motarsa da bindiga kirar Pump action. Ba tare kuma da gano musaabbin wannan kisan ba.
- Shugaban Argentina: Na Amince Da Shawarar Shugaba Xi Dake Da Nufin Inganta Ra’ayin Kasancewar Bangarori Da Dama
- An Gano Mage Mafi Tsufa A Duniya
Sannan kuma an nakalto cewa da yammacin ranar Juma’a ma ‘yan bindigan sun mamaye Mkpuma Akataka da ke karamar hukumar Izzi a jihar inda suka hallaka wasu mambobin jam’iyyar APC su biyu yayin da suke gudanar da taron tuntuba, lamarin da ya janyo bude musu wuta da har kuma wasu mutum biyu suka jikkata bayan wadanda aka kashe.
An nakalto cewa ‘yan bindigan da suka zo a kan Babur sun gudu bayan da suka aiwatar da aika-aikar tasu.
Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, Kwamandan rundunar tsaro ta Ebubeagu a jihar, Mr. Friday Ujoh, ya nuna matukar bakin cikinsu da damuwarsu bisa kai harin da wasu ‘yan bindiga suka yi kan jami’ansu.
Ya yi gargadin cewa ba za su dauki irin wannan mummunar aika-aikar ba, don haka ya gargadi masu kai Hare-haren da cewa su sauya matsayarsu.
Duk kokarin da wakilinmu ya yi domin jin ta bakin Kakakin hukumar ‘yansandan jihar Ebony, SP Chris Anyanwu, lamarin ya citura domin an Yi ta kiranka ya ki daga wayar zuwa aiko da wannan rahoton.