An jibge jami’an tsaro a sashen filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke a jihar Legas gabanin isowar shugaban kasa Muhammadu Buhari jihar.
Ana sa ran shugaban Buhari zai kaddamar da akin tekun Lekki wanda gwamnatin tarayya ta yi hadakar yin aikin da gwamnatin jihar da kuma wani kamfani da ake kira da Tolaram karkashin shirin aikin hadaka na PPP .
Har ila yau, ana sa ran shugaban zai kaddamar da kamfanin da zai iya casar shinkafa tan 32, wanda kuma ya kasance yana daga cikin manyan kamfanonin casar shinkafa a duniya.
Buhari zai kuma kaddamar da aikin hanya mai tsawon kilomita 18.75 da ke mahadar Eleko zuwa babbar hanyar Epe.
Bugu da kari, ana sa ran shugaban kasar zai kuma kaddamar da aiki na kashin farko na jirgin kasa na blue line sannan kuma zai kaddamar da aikin cibiyyar John Randle da aka gina don tunawa da tarihin al’adun kabilar Yarabawa.