Cibiyar Kula da Cututtuka Masu Yaduwa Ta Kasa (NCDC), ta tabbatar da cewa mutane 123 sun kamu da cutar sarkewar numfashi sannan 38 sun mutu a jihohi hudu.
Dokta Pricilla Ibekwe, Shugabar Sashen Ayyuka na Musamman da Hadin Gwiwa a NCDC, ce ta bayyana hakan a ranar Litinin a Abuja yayin taron Ministoci na mako-mako kan COVID-19 da ci gaba a fannin kiwon lafiyar kasar nan.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 4 A Bauchi
- NIS Ta Samu Gudunmawar Na’urorin Sadarwa Na Miliyoyin Nairori
Ibekwe, ta ce baya ga wadanda ake zargin sun kamu da cutar, akwai kuma wadanda gwaje-gwaje suka tabbatar sun kamu da cutar.
Ta ce hukumar ta NCDC tana aiki tare da ma’aikatun lafiya na Jihohi da abokan huldarsu domin sanya ido da kuma dakile barkewar cutar.
Ibekwe ta ce bisa sabbin rahotannin da aka samu daga jihohin da abun ya shafa, hukumar zuwa ranar 22 ga watan Janairu, an tabbatar da cewa mutane 123 ne suka kamu da cutar sannan 38 sun mutu a jihohi hudu.
Ta bayar da rahoton jihohi kamar haka: Kano – mutum 100 da aka tabbatar sun kamu da cutar kuma 32 sun mutu; Legas – mutum biyar sun kamu sai mutum uku da suka mutu; Yobe – mutum 17 ne suka kamu da cutar sannan uku sun mutu, yayin da Osun ta ba da rahoton bullar cutar kuma babu wanda ya mutu.
Ibekwe ta ce cutar sarkewar numfashi cuta ce mai hatsarin gaske wajen kawo tsaiko ga hanci, makogwaro, a wani lokaci ma har da fatar mutum.
A cewarta, cutar yana yaduwa cikin sauki tsakanin mutane ta hanyar hulda kai tsaye ko ta hanyar atishawa ko kuma mu’amala a tsakanin wanda ke dauke da cutar.