ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, July 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinubu Ba Shi Da Wani Tsari Na Taimaka Wa Arewa – Naja’atu

by Sulaiman
3 years ago
Tinubu

Ɗan takarar zama shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, bai shirya taimaka wa Arewa ta kowace fuska ba, a cewar tsohuwar jigo a jam’iyyar, Hajiya Naja’atu Mohammed.

Haka kuma ta ce Tinubu bai da isasshiyar lafiyar ƙwaƙwalwar da zai iya riƙe muƙamin shugabancin Nijeriya.

  • Sojoji Sun Dakile Harin ‘Yan Bindiga, Sun Kashe Da Yawa A Neja

Hajiya Naja’atu, wadda ‘yar asalin Kano ce, ta faɗi haka ne a wata hira da jaridar The Whistler ta yi da ita a ranar Lahadi.

ADVERTISEMENT

Hajiya Naja, kamar yadda ake kiran ta, an san ta da feɗe gaskiya komai ɗacin ta.

Ranar Asabar da ta gabata ne ta yi murabus daga rundunar yaƙin neman zaɓen Tinubu inda ta riƙe muƙamin darakta mai kula da ƙungiyoyin sa-kai.

LABARAI MASU NASABA

Zaɓen 2027: NNPP Ta Fara Shigar Da Sunayen ’Yan Takara, Ta Nemi INEC Ta Ƙara Mata Lokaci

ADC Ta Rushe Shugabannin Jam’iyyar A Kano, Ta Naɗa Kwamitin Riƙo

A wasiƙar murabus ɗin, wadda ta tura wa Shugaban APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, Naja’atu ta ce abubuwan da ke faruwa a cikin ‘yan kwanakin nan a fagen siyasar Nijeriya sun sanya ta ga cewa ba za ta iya ci gaba da yin siyasar kowace jam’iyya ba.

Ta ce ta gwammace ta taka rawar siyasar ta ta fuskar yin gwagwarmayar tabbatar da mulki mai nagarta don gyara ƙasar nan.

Sai dai kuma washegari, Lahadi, ta kai wa Atiku ziyara a gidan sa inda ta bayyana cewa ta koma goyon bayan takarar sa.

A hirar ta da jaridar The Whistler, ‘yar siyasar ta yi ƙarin bayani kan ainihin dalilan ta na barin Tinubu, ta ce ɗan takarar na APC ya bayyana ƙarara cewa ya na fama da ciwon mantuwa lokacin da ta ziyarce shi a London.

Ta ce: “Asiwaju da na zauna da shi, a yawancin lokacin duk barci ya ke yi, a gaskiya Bisi Akande ne na ke magana da shi. Abu mai muhimmanci shi ne ba wai kawai bai da ƙosasshiyar lafiyar jiki kaɗai ba ne, bai ma da lafiyar ƙwaƙwalwa. Ko mu na so, ko ba mu so, gaskiyar maganar kenan.

“Ba wai ba na ƙaunar sa ba ne, a’a, ina girmama shi domin na ji labarin mutum ɗaya ko biyu da ya taimaka wa a rayuwa, wanda hakan ya dace. To amma idan ka na zancen shugabancin sama da mutum miliyan ɗari biyu, ka san cewar idan ka cire ra’ayin ƙabilanci to ba zai iya ba, kawai wasu da ke zagaye da shi ne za su yi mulkin. Zahirin lamarin kenan. Ya na da taɓin hankali – ni na faɗa!

“Na zauna tare da shi tsawon awa biyu a London, idan ka yi maganar tsanwa, shi sai ya ba ka amsar ja. Ba ya ma iya raba ɗaya biyu. Ya na da tsananin ciwon mantuwa. Na tabbatar ya na da ciwon sankarar tsufa, wato Alzheimer’s, domin hatta kofin shayi bai iya riƙewa.

“Idan fa ka cire ra’ayin ƙabilanci, idan ka cire jaridun Legas da Ibadan, in da a ce Tinubu ba Bayarabe ba ne, to bai isa ya fito takarar zaɓe ba domin za su yi raga-raga da shi ne. To amma ga mutane nan jingim su na ta kare shi don kawai Bayarabe ne, ana faɗin ‘ai namu ne, egbe omo Oduduwa, hakan ya fi komai’.”

Hajiya Naja, wadda shekarun ta 66 a bana, ta ci gaba da cewa: “Tare da ni aka je kamfen na Yola, har sai da mu ka roƙe su da su karɓe makirfon daga hannun sa.

“Duk wani abu game da Tinubu an gina shi ne bisa ƙarya. Ka ɗauka cewar Bahaushe ne, shin zai iya yin takara da duk waɗannan matsalolin da ke tattare da shi? A wannan yaƙin neman zaɓen kada wanda ya yi maganar yaƙi da cin hanci da rashawa domin dukkan su su ne fuskar cin hanci da rashawar.”

Bugu da ƙari, Naja’atu Mohammed ta bayyana cewa Tinubu bai yi komai ba domin taimakon Arewa duk da ɗimbin matsalolin da su ka addabi yankin. Ta tuno da wata magana da ta yi masa a lokacin haɗuwar da ta yi da shi a London. Ta ce: “Na tambayi Tinubu, ‘Wane tanadi ka yi mana mu a Arewa?’ Sai ya kalle ni a tsabar ido na ya ce, “Ba wani abu.’ Na ce masa, ‘Ran ka ya daɗe, ka na nufin babu wani shiri da ka yi wa Arewa? Ga matsalar tsaro, yaran da ba su zuwa makaranta, aikin gona, da wasu masu yawa irin waɗannan, kowa a arewa-maso-gabas na jiran a kashe shi ko a yi kidinafin ɗin shi?”

A cewar ta, ita dai ba ta ƙara yin tozali da Tinubu ba tun daga lokacin da ta karɓi muƙamin da aka ba ta a rundunar yaƙin neman zaɓen sa.

Da aka tambaye ta ko ta na ganin Shugaba Muhammadu Buhari ya na goyon bayan Tinubu? Sai ta amsa da cewa: Buhari ba ya goyon bayan kowa; son ran sa ya yi yawa, ka ce Ni na faɗa maka, Buhari bai taɓa goyon bayan kowa ba sai kan sa kaɗai.

“Zan yi matuƙar mamaki idan ya na goyon bayan shi, kuma idan Buhari na goyon bayan wani to babu abin da wannan mutum zai samu. Saboda haka, da na ji Asiwaju ya ce zai ɗora a inda Buhari ya tsaya, cewa na yi, ‘Ka kashe kan ka a Arewa’ saboda ba a son Buhari. Je ka duba kasafin kuɗin sa a tsawon shekarun nan, abin da ya fi ware wa kuɗi mafi girma a arewa-maso-yamma shi ne kashi 12 cikin ɗari, kuɗin da ya fi ware wa harkar gona shi ne kashi 2, kuma ana ƙin jinin sa saboda bambancin da ya ke nunawa. Dukkan hafsoshin soja da ‘yan sanda, har da hukumar kwana-kwana, ‘yan Arewa ya naɗa, kuma sai ya naɗa marasa amfani daga cikin su, saboda a ci gaba da kashe mu don ka riƙa cewa ɗan’uwan ka ne ke kashe ka. To, idan ɗan’uwan ka ne ke kashe ka menene bambancin ga wanda abin ya shafa? Yanzu maganar da ake yi, ana can ana sace mutane a Katsina, babu ranar da ba a sace mutane a jihohin Katsina da Zamfara da Neja. Saboda haka, idan an ce Fulani ko ba Fulani ba ne, wa ya damu? Idan daga sama ka faɗo amma kai shugaba ne da ya cancanta, mecece samuwar a wurin da ya dace?

“Amma Nijeriya ta zama mallakin masu mulki. In da a ce Osinbajo aka tsayar, na rantse da Allah da na ba da rayuwa ta saboda Osinbajo, domin shi ne ya fi cancanta, mutum ne a buɗe, ya na da himma, kuma ya na saka ido a kan komai sannan ya na kallon Nijeriya baki ɗayan ta. A ‘yan watannin da ya riƙe ƙasar, ya canja abubuwa da dama. Saboda haka, saboda me zan saka ra’ayin son zuciya. In da Yarabawa da gaske su ke me ya sa ba su kawo Osinbajo ba, wanda fasto ne? Ka zo ka na tikitin Muslim-Muslim a yanzu. Annabi mai tsira da aminci ya ce kafiri ya fi Musulmin da bai yin adalci. To, don me zan damu da wani Muslim-Muslim? To amma sun dage wajen yin gangamin mutane a fagen siyasa amma kuma su na yaudarar jama’a ne. Wane Musulunci su ke yi? Mutumin da ko Fatiha bai iya karantawa, shi ke kiran kan shi Musulmi. Idan ba ka karanta Fatiha ba, ba ka da sallah, wanda ya nuna ba ya ma sallah kenan. Wane irin shashanci ne wannan? Ba ruwa na da wani zancen tikitin Muslim-Muslim, to amma saboda Nijeriya ƙasa ce ta jahilci, an kai tumaki mayanka, shi ya sa masu mulki su ka hana ‘ya’yan talaka su yi ilimi, musamman a Arewa.”

Hajiya Naja ta bayyana cewa ita yanzu ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, wato Atiku Abubakar, za ta goya wa baya a zaɓen da za a yi domin gara shi da Tinubu.

Ta ce: “Abin da zan ce shi ne idan aka ce in zaɓi ɗayan biyu a tsakanin wani mugun abu da wani mugun abin, to Atiku zan bi, domin kuwa ko ba komai dai na bi inda hankali na zai kwanta. Ba domin son rai na na ke yi ba, ina yi ne saboda Allah kuma saboda ƙasa ta.”

Tinubu
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Iran Da Su Aiwatar Da Cikakkiyar Takardar Bayanin Fahimtar Juna Da Aka Cimma
  • Sulaiman
    Sin Ta Yi Kira Da A Cike Gibin Cin Gajiyar Fasahar AI
  • Sulaiman
    Ministan Lafiya Na DRC Ya Gode Wa Sin Bisa Tura Kwararrun Likitoci Kasar Don Tallafa Wa Dakile Ebola
  • Sulaiman
    Sin Ta Yi Watsi Da Ikirarin Philippine Kan Tekun Kudancinta

MASU ALAKA

Zaɓen 2027: NNPP Ta Fara Shigar Da Sunayen ’Yan Takara, Ta Nemi INEC Ta Ƙara Mata Lokaci
Siyasa

Zaɓen 2027: NNPP Ta Fara Shigar Da Sunayen ’Yan Takara, Ta Nemi INEC Ta Ƙara Mata Lokaci

July 8, 2026
ADC Ta Rushe Shugabannin Jam’iyyar A Kano, Ta Naɗa Kwamitin Riƙo
Manyan Labarai

ADC Ta Rushe Shugabannin Jam’iyyar A Kano, Ta Naɗa Kwamitin Riƙo

July 6, 2026
Jam’iyyar PDP Ce Za Ta Dawo Da Kwanciyar Hankali A Nijeriya – Hajiya Khadija
Siyasa

Jam’iyyar PDP Ce Za Ta Dawo Da Kwanciyar Hankali A Nijeriya – Hajiya Khadija

July 5, 2026
Next Post
Magoya Baya Sun Shiga Hannu A Uganda Bayan Arsenal Ta Doke Manchester United

Magoya Baya Sun Shiga Hannu A Uganda Bayan Arsenal Ta Doke Manchester United

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Iran Da Su Aiwatar Da Cikakkiyar Takardar Bayanin Fahimtar Juna Da Aka Cimma

Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Iran Da Su Aiwatar Da Cikakkiyar Takardar Bayanin Fahimtar Juna Da Aka Cimma

July 8, 2026
Sin Ta Yi Kira Da A Cike Gibin Cin Gajiyar Fasahar AI

Sin Ta Yi Kira Da A Cike Gibin Cin Gajiyar Fasahar AI

July 8, 2026
Kotu Ta Tsare Malamin ABU Kan Zargin Gwamnatin Katsina Da Ɗaukar Nauyin Aikin Hajjin ‘Yan Bindiga

Kotu Ta Tsare Malamin ABU Kan Zargin Gwamnatin Katsina Da Ɗaukar Nauyin Aikin Hajjin ‘Yan Bindiga

July 8, 2026
Ministan Lafiya Na DRC Ya Gode Wa Sin Bisa Tura Kwararrun Likitoci Kasar Don Tallafa Wa Dakile Ebola

Ministan Lafiya Na DRC Ya Gode Wa Sin Bisa Tura Kwararrun Likitoci Kasar Don Tallafa Wa Dakile Ebola

July 8, 2026
Sin Ta Yi Watsi Da Ikirarin Philippine Kan Tekun Kudancinta

Sin Ta Yi Watsi Da Ikirarin Philippine Kan Tekun Kudancinta

July 8, 2026
Sin Da Tanzania Da Zambia Sun Karrama Jaruman Sinawa A Bikin Cika Shekaru 50 Da Kafa Layin Dogo Na TAZARA

Sin Da Tanzania Da Zambia Sun Karrama Jaruman Sinawa A Bikin Cika Shekaru 50 Da Kafa Layin Dogo Na TAZARA

July 8, 2026
Zaɓen 2027: NNPP Ta Fara Shigar Da Sunayen ’Yan Takara, Ta Nemi INEC Ta Ƙara Mata Lokaci

Zaɓen 2027: NNPP Ta Fara Shigar Da Sunayen ’Yan Takara, Ta Nemi INEC Ta Ƙara Mata Lokaci

July 8, 2026
Damar Fita Daga Kangin Dalar Amurka Ta Sake Samuwa Ga Kasashen Afirka

Damar Fita Daga Kangin Dalar Amurka Ta Sake Samuwa Ga Kasashen Afirka

July 8, 2026
Badaƙalar PFIPC: Ban Taɓa Haɗuwa Da Gbajabiamila Ba – Adeyemi

Badaƙalar PFIPC: Ban Taɓa Haɗuwa Da Gbajabiamila Ba – Adeyemi

July 8, 2026
NNGF Ta Kaddamar Da Kwamitin Amintattu Na Gidauniyar Asusun Tsaro Ta Yankin

NNGF Ta Kaddamar Da Kwamitin Amintattu Na Gidauniyar Asusun Tsaro Ta Yankin

July 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.