Rahotanni daga kasar Brazil sun bayyana cewa za’a yi gwanjon rigar marigayi Pele mai lamba 10 ta tawagar kwallon kafar Brazil ta karshen wasansa a kwallon kafa a kan kudi fam dubu talatin (30,000).
Rigar dai daya ce daga cikin riguna biyu mai lamba 10 da aka yi a wasan Brazil da Yugoslabia a shekarar 1971, in ji kamfanin gwanjon, Hansons, sai dai Pele bai sa rigar ba a wasan, amma ya bayar da ita kyauta ga Abilio Jose de Silba da ake kira Nocaute Jack, wanda ya yi aiki da tawagar Brazil tsakanin shekarar 1960 zuwa 1994.
- ’Yar Kasuwa Elizabeth Homes: Labarin Tashe Da Rushewarta (II)
- Naja’atu: Cikon Banci Ce A Wurinmu, Tun Da Muka Kore Ta Take Ta Sambatu – APC
Daga baya ne wani mai gidan abinci a Shropshire ya sayi rigar, wanda ya yi fatan za a ajiye ta a dakin adana kayan tarihi kuma tun daga wancan lokacin aka ajiye rigar har kawo yanzu.
Wani mai shekara 33, wanda ba ya son a bayyana sunansa ya ce ya sayi rigar a shekarar 2020 daga wani mai tara tsoffin abubuwan tarihi a fannin kwallon kafa kuma za’a sayar da rigar ranar 15 ga Fabrairu mai zuwa.
Pele ya ci kwallo 1,281 a wasanni1,363 a shekara 21 da ya yi yana buga kwallon kafa, har da kwallaye 77 da ya ci wa Brazil a wasanni 92 sai dai tuni dan wasa Neymar ya kamo kwallayen na Pele.
Pele ya mutu a watan Disambar shekarar da ta gabata ta 2022 kuma shi ne dan wasa tilo da ya lashe kofin duniya karo uku, an karrama shi da kyautar fitatcen dan kwallon duniya a karni da aka yi masa a 2000.