Jigon jam’iyyar PDP a karamar hukumar Makarfi, Alhaji Magaji Jarman Makarfi ya ce matsalolin da jam’iyyar APC ta jefa mutanen Nijeriya ya kamata su zama darasi, musamman a zabukan da ke zuwa.
Jarman ya ce zabukan da za su zo dama ce ga al’ummar kasar nan ta sauya gwamnati APC da ta jefa su cikin halin tsaka-mai-wuya a fannin rayuwa daban-daban.
Ya ce zabuka ne wadanda ke da matukar muhimmanci domin da su ne za su sake sauya fasalin kasar nan bayan sun kwace milki daga APC.
Jarma ya tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa suna da kyawawan tsare-tsare da za su taimaka wajen farfado da rayuwar al’ummar kasar nan daga halin wahalar da aka jefa su ciki.
Ya yi waiwaye kan lokacin da jam’iyyar PDP ke kan karagar milkin kasar nan wanda ya ce, al’umma kansu za su iya zama shaida kan irin yadda rayuwa ke da sauki, wanda kuma a halin yanzu za a iya cewa ana cikin mawuyacin hali wanda.
A cewarsa, dukkan wadannan matsalolin sun faru ne sakamakon rashin iya tafiyar da amanar kasa da aka dankata a hannun masu milki a karkashin jam’iyyar APC.
Don haka, sai Jarman ya ce yanzu dai dabara ta rage ga mai shiga rijiya, zai zabi APC ne ya ci gaba da yin kasa, ko ko zai zabi PDP domin ya farfado?