Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Dai Bing ya yi kira ga al’ummar kasa da kasa a jiya Jumm’a cewa, da su taimaka wa kasar Mali kara karfinta na yaki da ta’addanci, sannan ba da tallafi a fannonin kudade da kayayyaki da bayanai da sauransu, da mutunta ikon Mali na yin hadin gwiwar tsaro da sauran kasashen duniya.
A wannan rana, a yayin bude taro kan batun tsaron Mali da kwamitin tsaron MDD ya kira, Dai Bing ya bayyana cewa, a baya-bayan nan, Mali ta gudanar da ayyukan yaki da ta’addanci a cikin yankuna kamar Mopt da sauran yankunan kasar, domin tabbatar da zaman lafiya a kasar da kare tsaron fararen hula, wadannan ayyuka sun cancanci yabo sosai. A halin yanzu, shirin samar da zaman lafiya na siyasan Mali yana cikin lokaci mai muhimmanci, don haka bai kamata al’ummar kasa da kasa su rage yadda suke mai da hankali da nuna goyon baya ga Mali ba, kamata ya yi sa taimakawa gwamnatin Mali wajen tinkarar kalubaloli a dukkan fannoni.
Dai Bing ya kara da cewa, yanayin tattalin arzikin Mali ba ya da kyau, kuma kashi daya bisa hudu na al’ummar kasar suna bukatar tallafin jin kai. Ya kamata kasa da kasa su hada kai don taimaka wa Mali don magance matsaloli dake damunta, da tabbatar da samar da isashen tallafin kudi, da kaucewa aukuwar bala’in jin kai a kasar Mali.
Ya zama wajibi a kara tallafin da ake baiwa Mali, ta yadda za ta samu zarafin aiwatar da ayyuka a fannonin bunkasa aikin gona da gina ababen more rayuwar jama’a da ilimi, da kiwon lafiya, da taimakawa Mali kara karfinta na dogara da kanta wajen neman ci gaba. (Safiyah Ma)