Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana alhininsa game da rasuwar Dakta Nuhu Sanusi, Sarkin Dutse a Jihar Jigawa.
A cikin sakon ta’aziyyar da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Talata a Abuja, shugaban ya ce marigayin na daya daga cikin shugabannin Arewacin Nijeriya na zamani.
- Kaddamar Da Muhimman Ababen More Rayuwa A Najeriya Ya Bude Sabon Babi A Fannin Hadin Gwiwar Sin Da Afirka
- Cikin Shekaru 3 Da Suka Gabata Sin Ta Yi Rawar Gani A Fannin Yaki Da Annobar COVID-19
Kafin rasuwarsa, Sarkin ya kasance Shugaban Jami’ar Jihar Sakkwato.
Shugaban ya yi nuni da cewa, an dauki Sarkin a matsayin jagora sannan abin koyi a duniya wajen ci gaban rayuwa, kuma mai fafutukar kare gandun daji da korayen halittu.”
Yayin da yake bayyana alhinin rasuwar Sarkin, Buhari ya ce, “Ya taimaka matuka wajen ci gaban garin Dutse cikin shekaru 30 da suka gabata a karkashin mulkinsa.
“Shi mutum ne mai zaman kansa wanda kowa ke so.”
Buhari ya aike da ta’aziyyarsa ga Masarautar Dutse, gwamnati da al’ummar Jihar Jigawa bisa wannan rashi da aka yi.