Sanata Smart Adeyemi, ya bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da ya roki gafarar ‘yan Nijeriya maimakon neman kujerar shugaban kasa.
Adeyemi, wanda ke wakiltar Kogi ta Yamma a Majalisar Dokoki, ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da ’yan asalin Jihar Kogi mazauna Minna a ranar Talata a wani taron mara wa Tinubu da Shettima baya.
- Cikin Shekaru 3 Da Suka Gabata Sin Ta Yi Rawar Gani A Fannin Yaki Da Annobar COVID-19
- Emefiele Ya Bayyana A Gaban Majalisa Kan Sauya Fasalin Kudi
Ya ce ya kamata tsohon mataimakin shugaban kasar ya nemi afuwar ‘yan Nijeriya kan sayar da dukiyar kasa baki daya.
“Atiku karkashin kulawarsa a matsayinsa na shugaban kamfanonin kasuwanci, ya sayar da dukiyoyinmu na gama-gari, kuma shi ne tushen talauci da rashin tsaro a Nijeriya.
“Don haka Atiku ya kamata ya fara bai wa ‘yan Nijeriya hakuri kan yadda suka kashe Naira biliyan 16 don samar da wutar lantarki amma ba mu da wutar lantarki ta sa’o’i 24.
“Ya kamata Atiku ya bayyana mana irin yadda suka karkatar da dukiyar gwamnati wanda ko shakka babu ya hada da rashin tsaro da tattalin arzikin Nijeriya a yau sakamakon aika-aikar da PDP ta yi wanda Atiku Abubakar ya jagoranta,” in ji shi.
Sai dai Sanatan ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su marawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu da Kashim Shettima baya ya kara da cewa dukkansu mutane ne masu gaskiya.
“Abin da Nijeriya ke bukata a yanzu shi ne mutum mai hangen nesa ta yadda za a inganta rayuwarmu, ta yadda za mu ci moriyar tsaron rayuka da dukiyoyi da kuma tattalin arzikin kasar nan ya kai wani matsayi mai girma,” in ji shi.
Ya bayyana Tinubu da Shettima a matsayin wani babban hadin kai.
A nasa jawabin, Gwamna Abubakar Sani-Bello na Jihar Neja, ya yi tir da halin da kasar nan ke ciki idan ya kwatanta shi da yadda ta kasance kafin shekarar 1999, ya kuma shawarci ‘yan Nijeriya da su zabi shugabannin da suka cancanta da za su fitar da kasar nan daga halin da ta ke ciki.
“Halin da Nijeriya ke ciki kafin 1999 da abin da yake faruwa a yanzu ya sa na koka kan makomar ‘ya’yanmu.
“Amma yanayin da muke ciki a yau abun bakin ciki ne kuma abin da Nijeriya ta kasance a yau yana da matukar tausayi,” in ji shi.
Bello ya yaba wa al’ummar Kogi mazauna jihar tare da yin kira a gare su da sauran wadanda ba ‘yan asalin jihar ba da su mara wa jam’iyyar APC baya su zabi duk ‘yan takararta.
A nasa jawabin, Sarkin Ebira a Neja, Alhaji Mansu Abdul, ya yi alkawarin bayar da cikakken goyon baya ga dukkan ‘yan takarar jam’iyyar APC a matakin jiha da kasa baki daya.
Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN), ya rawaito cewa taron ya kuma shaida rabon kayan aiki ga mutanen Kogi mazauna Neja.