• English
  • Business News
Wednesday, October 29, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yansanda Sun Kama Mutum 2 Kan Zargin Sace Kananan Yara 2 A Kano

by Sadiq
3 years ago
'Yansanda

Rundunar ‘yansandan Jihar Kano, ta tabbatar da cafke wasu mutane biyu da ake zarginsu da sace wasu kananan yara biyu tare da kubutar da yaran daga hannunsu.

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Abdullahi Haruna-Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kano ranar Talata.

  • NIS Ta Samar Da Fasfo Kimanin Miliyan 2 A Shekarar 2022 —Gwamnatin Tarayya
  • Mataimakin Wakilin Kasar Sin Dake MDD Ya Yi Kira Ga Kasashen Duniya Da Su Taimakawa Mali Kara Karfin Yaki Da Ta’addanci

Wadanda ake zargin sun hada da Nura Auwal mai shekaru 22 da ke unguwar Rijiyar Lemo a Kano da Abubakar Lawal mai shekaru 22 daga unguwar Bachirawa a Kano.

“A ranar 26 ga watan Janairu, mun samu labari daga Isyaku Salisu da Auwal Sale mazauna Bachirawa a Karamar Hukumar Ungogo a Kano, cewa an yi garkuwa da ‘ya’yansu Umar Isyaku mai shekaru 3 da Aliyu Auwal mai shekaru 4.

“An aika musu da sakon waya da bayanan asusun banki, inda suka nemi a biya su Naira miliyan 20, amma daga baya suka biya Naira miliyan biyu kan kowane yaro.

LABARAI MASU NASABA

JIBWIS Ta Miƙa Takardar Koke Ga Gwamnatin Kaduna Kan Zargin Wasu Malamai Da Yunƙurin Tada Husuma

Zamfara Ta Fara Sauyawa Zuwa Jihar Fasahar Zamani, In ji Gwamna Lawal

“Da samun rahoton kwamishinan ‘yansandan jihar, Mista Mamman Dauda, ​​ya umurci rundunar ‘Operation Restore Peace’ karkashin jagorancin SP Aliyu Auwal, jami’in da ke kula da masu garkuwa da mutane, sashen binciken manyan laifuka na jihar, da su kubutar da wadanda aka sace tare da kamo wadanda suka aikata laifin.

“An ceto wadanda abin ya shafa ba tare da sun ji rauni ba a wani gini da ba a kammala ba.”

Ya kara da cewa wadanda ake zargin sun amsa cewa sun hada baki ne suka yi garkuwa da yaran biyu tare da aika wa iyayensu sakon waya kan neman kudin fansa.

Kakakin ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

JIBWIS Ta Miƙa Takardar Koke Ga Gwamnatin Kaduna Kan Zargin Wasu Malamai Da Yunƙurin Tada Husuma
Labarai

JIBWIS Ta Miƙa Takardar Koke Ga Gwamnatin Kaduna Kan Zargin Wasu Malamai Da Yunƙurin Tada Husuma

October 28, 2025
Zamfara Ta Fara Sauyawa Zuwa Jihar Fasahar Zamani, In ji Gwamna Lawal
Labarai

Zamfara Ta Fara Sauyawa Zuwa Jihar Fasahar Zamani, In ji Gwamna Lawal

October 28, 2025
Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Ajali Tare Da Jikkata Wasu A Gombe
Labarai

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Ajali Tare Da Jikkata Wasu A Gombe

October 28, 2025
Next Post
Kashi 50 Na Magungunan Afrika Jabu Ne – Majalisar Dinkin Duniya

Kashi 50 Na Magungunan Afrika Jabu Ne - Majalisar Dinkin Duniya

LABARAI MASU NASABA

Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Bude Kofa Da Karfafa Daidaita Dabarun Samar Da Ci Gaba

Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Bude Kofa Da Karfafa Daidaita Dabarun Samar Da Ci Gaba

October 28, 2025
JIBWIS Ta Miƙa Takardar Koke Ga Gwamnatin Kaduna Kan Zargin Wasu Malamai Da Yunƙurin Tada Husuma

JIBWIS Ta Miƙa Takardar Koke Ga Gwamnatin Kaduna Kan Zargin Wasu Malamai Da Yunƙurin Tada Husuma

October 28, 2025
An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu

An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu

October 28, 2025
Zamfara Ta Fara Sauyawa Zuwa Jihar Fasahar Zamani, In ji Gwamna Lawal

Zamfara Ta Fara Sauyawa Zuwa Jihar Fasahar Zamani, In ji Gwamna Lawal

October 28, 2025
Masanan Kasar Sin Da Afirka Sun Hada Karfi Da Karfe Don Habaka Samun Wadatar Abinci Da Zamanantar Da Aikin Gona

Masanan Kasar Sin Da Afirka Sun Hada Karfi Da Karfe Don Habaka Samun Wadatar Abinci Da Zamanantar Da Aikin Gona

October 28, 2025
Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Ajali Tare Da Jikkata Wasu A Gombe

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Ajali Tare Da Jikkata Wasu A Gombe

October 28, 2025
Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin

Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin

October 28, 2025
Kano Ta Bai Wa Mata 5,200 Tallafin Naira Miliyan 260

Kano Ta Bai Wa Mata 5,200 Tallafin Naira Miliyan 260

October 28, 2025
An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas

An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas

October 28, 2025
Gwamna Bago Ya Amince Da Biyan Karin Albashin Naira 20,000 Ga Ma’aikata 

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Hutun Kwanaki 2 Don Zaɓen Ƙananan Hukumomi

October 28, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.