• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dalilan Da Ke Hana Kwamfuta Da Wayoyin Hannu Sauri

by Ibrahim Sabo
3 years ago
Kwamfuta

Wannan rubutu na yi shi ne saboda korafe-korafen jama’a masu ta’ammuli da na’urorin Kwamfuta da manyan wayoyin hannu da kullum ake amfani da su domin gudanar da al’amuran yau da kullum.

Ta’ammuli da Kwamfuta ko wayar hannu ya zamo jigo a rayuwar jama’a domin gudanar da aiyukan yau da kullum, kama daga kasuwanci, fannin ilimi, fannin lafiya, bincike-bincike, fannin tsaro, ayyukan kotu, fannin yada labarai da sauran al’amura masu yawan gaske.

  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Tir Da Kisan Fulani 40 A Jihar Nasarawa

Ilimin sarrafa kwamfuta da wayar hannu ya zama mai saukin gaske. Ganin yadda ake ta kara inganta su da kuma saukaka fahimtar yadda za’a sarrafa su ko da mutum ba shi da ilimin zamani a halin yanzu, za a ga kusan kowa yana da wayar hannu ko kwamfuta koma dukkansu biyu, babu babba babu yaro.
Yawaitar amfani da na’urori domin bukatun yau da kullum, yana da alaka da saukin mallakarsu, ko da yake masu iya magana sunce, iya kudinka iya shagalinka. Dukkanin wadannan na’urori sun yi tarayya wajen abubuwa kamar haka; saurin sarrafa aiki, rumbun adana abubuwa ko kayan da aka sarrafa, ababen dogaro lokacin gudanar da aiki, saukin dauka ko rikewa a hannu lokacin zirga-zirga da sauran al’amura.

Idan ba a samu abubuwa biyu zuwa uku daga cikin wadancan siffofi da na bayyana ba, yakan haifar da damuwa wajen sarrafa na’ura. Kwamfuta da wayar hannu sukanyi nauyi ko jinkiri wajen sarrafa aiyuka, saboda dalilai masu yawa. Amma zan yi bayani a kan wadanda suka fi muhimmanci.

Akwai cutar na’ura mai yaduwa (Birus), sanin kowane cutar na’ura ta bairos da ire-irensu suna taka rawa wajen sauya akalar sarrafa na’ura, sukan cutar da ita, suna hana ta yin aiki kamar yadda aka tsara ta, sai taki gaba taki baya. Amfani da manhajar maganceta (anti-birus) yana da matukar muhimmanci.

LABARAI MASU NASABA

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

Wasu sukan cunkushe na’ura da manhajoji ba bisa ka’ida ba. Akwai wadanda suke akidar saka manhajoji iri-iri masu yawa ko da basu iya aiki da su ba. Yin hakan yana haddasa cunkushewar rumbun adana aiki (memory). Saboda cire manhajar da ba’a amfani da ita yana bunkasa aikin na’ura cikin sauri.

Yin amfani da na’ura a cikin yanayi mai zafi ko waje maras isashshiyar iska yana haddasawa sassan ita na’urar jinkirin aiki. Wanda hakan yana jawo koma baya ga ingancin na’ura.

Dan haka idan babu na’urar sanyaya daki sai a kunna fanka, idan ita ma babu to sai a bude kofofi da wunduna domin iska ta dinga ratsa su a lokacin da ake aiki.

Idan ba a sabunta manhajoji a kan lokaci, to wannan ma babban al’amari ne da yake jawo tarnaki ga na’ura. Sabunta manhaja (update) a kan lokaci yana da amfani domin yana magance duk wata matsala tattare da ita kanta manhajar da sauran sassan na’ura dake aiki da manhaja lokacin gudanar da aiki.

Yin amfani da gurbatattun manhajoji (applications) na da illa ga na’ura. Domin yakan yi sanadiyyar bude dukkan kofofin sirri na na’ura domin cututtuka masu yawa su shiga. Kuma sukan zamo makamai da masu kutse ke amfani dasu wajen cutar da al’umma. Kuma an fi samun su a manhajoji na kyauta (free).

Amfani da sahihan manhajoji shi ne mafi da cewa ga jama’a.
Barin datti ko kura a cikin na’ura, wato rashin tsaftace na’ura ko dakunan da ake amfani da ita, harma da teburin da aka dorata idan ta girke ce (desktop), yana da matukar illa wajen toshe kofofin shakar iska ga ita na’urar, har ma lalacewar wasu sassa saboda tsabar datti da kura. Saboda haka kula da tsaftar na’ura yana inganta sassanta yadda za ta yi aiki cikin sauki.

Fuskantar katsewar wutar lantarki a lokacin da ake tsakiyar aiki da na’uara, ko kwamfuta ta mutu saboda batir babu isashshen caji, babbar matsalace.

Hakan yana haddasa matsala ga rumbun adana aiki (Hard Disk Dribe) kuma yana haddasa jinkiri wajen gudanar da aiyuka. Amfani da na’urar adana wutar lantar ki (UPS) da kuma isashshen caji ga wayoyi ko kwamfuta Laptop, zai taimaka kwarai. Ana so idan an dauke wuta sai a kashe a hakura har sai an sami wuta ko kuma a tayar da Janareto.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mun Dakile Hari A Kano Da Ka Iya Zama Mafi Muni A Tarihin Nijeriya —Irabor
Rahotonni

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

October 17, 2025
Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya
Rahotonni

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

October 11, 2025
Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki
Rahotonni

Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki

October 11, 2025
Next Post
Sin Na Matukar Adawa Da Matakin Amurka Na Harbo Babban Balan-balan Din Kasar Sin

Sin Na Matukar Adawa Da Matakin Amurka Na Harbo Babban Balan-balan Din Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Majalisar Dattawa

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025
Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

November 5, 2025
Gwamna Yusuf

Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu

November 5, 2025
An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

November 5, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisa Ta Nuna Damuwa Kan Rahoton Yiwuwar Asarar Dala Biliyan 300 A Badaƙalar Ɗanyen Mai

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.