Jami’an Hukumar EFCC sun kama wani manajan harkokin gudanarwa na wani babban bankin kasuwanci a Abuja ranar Litinin kan laifin kin sanya kudi a na’urorin ATM na bankin da yake duk da cewa yana da cabar kudi naira miliyan 29 cikin sabbin kudade a rumbun ajiyar bankin.
Gabanin Jami’an hukumar su tafi da shi don ci gaba da amsa tambayoyi sun bayar da umarnin a sanya kudade a dukkan na’urorin ATM din don jin dadin kwastomomin da suke da bukatar kudaden, wadanda suka shafe sa’o’i suna bin layi ba tare da samun sabbin takardun kudaden ba.
- Zaben APC: Jami’an Hukumar EFCC Sun Yi Tsinke Filin APC Don Sanya Ido Kan Hadadar Kudi
- EFCC Ta Cafke Wani Dan Siyasa Da Wasu Kan Satar Kudin Banki N1.4bn A Jihar Kogi
Sama da rassan bankuna biyar ne jami’an suka gudanar a Abuja ranar Litinin. Ana ci gaba da gudanar da irin wannan aiki a fadin kasar.
Za a ci gaba da gudanar da aikin har sai an dawo da tsarin banki kamar yadda aka saba.
Hukumar EFCC ta kara da cewa ‘Yan Nijeriya na shan wahala wurin samun kudadensu a kowane banki.
Hukumar ta bukaci Jama’a da su kai rahoton duk wadanda ake zargi da aikata ba daidai ga hukumar, domin kawo dauki.