Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), ta kwato katunan zabe 106 daga hannun wasu bakin haure waje mazauna Jihar Kwara.
Kwanturolan NIS a jihar, Aminu Shamsuddin ne ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), a ranar Litinin.
- Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Dakatar Da CBN Da Buhari Ƙara Wa’adin Maye Tsoffin Kuɗi
- Tawagogin Sinawa Masu Yawon Shakatawa Sun Sake Fara Ziyara A Ketare
Shamsuddin ya ce an kama wasu bakin haure da katunan zaben Nijeriya a lokacin da jami’an shige-da-fice suka gudanar da sintiri a cikin babban birnin Ilorin.
Ya ce NIS ta wayar da kan dukkan baki ‘yan kasashen waje dokokin da suka dabaibaye zabe tare da gayyatarsu domin wayar musu da kai game da hukuncin da ke jiran wadanda suka karya doka.
Ya ce: “A daya daga cikin tattaunawar wayar da kan jama’a, ‘yan kasashen waje sun tsorata da jin cewa duk wanda aka kama yana taka rawa a lokacin zaben Nijeriya za a daure shi, a mayar da shi kasarsa sannan a shafa masa bakin fenti.
“Wasu daga cikinsu da ke da katin zabe na Nijeriya sun dawo da shi tare da neman afuwa.
“Yawancin wadanda suka aikata wannan aika-aika matasa ne maza da mata, daga Jamhuriyar Nijar, Jamhuriyar Benin da kuma Ghana.
“Sun yi ikirarin cewa iyayen gidansu ne suka karfafa musu gwiwa da su yi katin zabe da kuma kada kuri’a a lokacin zaben, domin su karawa ‘yan takararsu yawan kuri’u.”
Kwanturolan ya yi gargadin cewa duk wanda aka kama da katin zaben za a daure shi, tare da mayar da shi gida sannan a sanya masa takunkumi, wanda hakan ke nufin ba za a sake bari ya shigo Nijeriya ba.