Dandazon jama’a da dama sun taru don gudanar da zanga-zangar lumana a kan babbar hanyar Ore-Benin a Jihar Ondo, don nuna rashin jin dadinsu kan rashin kudi da kuma karancin man fetur.
Masu zanga-zangar da suka fusata sun tare hanyar wanda hakan ya haifar da cunkoson ababen hawa.
- Duniya Ta Shiga Alhinin Mutuwar Sama Da Mutum 3,000 A Turkiyya Da Siriya
- Yadda Aka Yi Wa ‘Yan Nijeriya 16 Kisan Gilla A Burkina Faso
Matafiya da dama da ke bin hanyar sun makale na sa’o’i da dama.
Daya daga cikin masu zanga-zangar, Adebayo Adeyemi, ya ce wahalhalun da ‘yan Nijeriya ke fuskanta a baya-bayan nan a fadin kasar nan abin ban tsoro ne.
“Muna zanga-zangar ne don aika sako ga gwamnati, cewa mu talakawa muna shan wahala,” in ji Adeyemi.
Cikakken bayani na tafe…