Ana zargin wani mai suna Ibrahim Dauda, bisa hallaka dan uwansa mai suna Tunde bayan da fada ya kaure a tsakaninsu kan Naira 1,000.
Sun dai bai wa hammata iska ne a gidansu da ke a kan titin Amusa a unguwar Obadore a yankin Igando, da ke Jihar Legas.
- Zanga-Zanga Ta Barke A Ondo Kan Karancin Kudi Da Man Fetur
- Karancin Mai: Kungiyoyin Sufuri Za Su Yi Zanga-Zanga A Hedikwatar NNPC
An ruwaito cewa, rikicin ya barke ne a tsakanin ‘yan uwan biyu a kan Naira 1,000.
Ana zargin Ibrahim ya dauki rodi ya rabka wa Tunde dan shekara 27 a goshi, inda aka garzaya da shi Babban Asibitin Igando, inda likita ya tabbatar da mutuwarsa.
Wata majiya ta ce, fadan nasu ya auku ne a ranar 25 ga watan Janairu 2023.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, kakakin rundunar ‘yansandan jihar,
SP Benjamin Hundeyin, bai fitar da wata sanarwar kan faruwar lamarin ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp