Kungiyar Jaruman wasan kwaikwayo ta kasa (AGN), ta dakatar da jarumin masana’antar shirya fina-finai na Kudancin Nijeriya, Moses Armstrong, har illa masha Allah, sakamakon zarginsa da da yi wa wata karamar yarinya’yar shekara 16 fyade a jihar Anambra.
Shugaban kungiyar ta AGN ta kasa, Emeka Rollas, ne ya sanya hannu kan takardar dakatarwar.
- ‘Yan Sanda Sun Cafke Jarumin Nollywood Kan Zargin Yi Wa Karamar Yarinya Fyade
- Yansanda A Jihar Borno Sun Kama Tsoho Mai Shekara 80 Da Laifin Yi Wa ‘Yar Shekara 11 Fyade
Ameka Rollas, ya yi bayanin cewar dakatarwar ta dundundun ta zama wajibi saboda a ba Jami’a damar gudanar da bincike domin tabbatar da hakikanin abun da ya faru kan zargin da ake masa.
Sanarwar da daraktan yada labarai na kungiyar, Monalisa Chind ya fitar wa manema labarai a ranar Asabar cewa, “Kwamitin Majalisar koli na kungiyar AGN ta yanke hukuncin dakatar da Moses Armstrong sakamakon cafke shi da ‘yan sanda suka yi kan zargin yi wa karamar yarinya fyade.
“Takardar dakatarwar shugaban kungiyar
Ejezie Emeka Rollas, ne da kansa ya sanya mata hannu bisa kwararan hujjoji da aka tattaro a binciken farko-farko da kungiyarmu ta gudanar kan batun.