Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso ya bayyana ce babu wani dan Nijeriya mai hankali da zai zabi APC ko PDP a ranar 25 ga watan Fabrairu lokacin da za a gudanar da zaben shugaban kasa.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a ranar Litinin lokacin da yake jawabi gaban dimbin magoya bayansa a wurin gangamin yakin neman zaben gwamna a kara-mar hukumar Tarauni da ke Jihar Kano.
Tsohon gwamnan Jihar Kano ya siffanta shugabancin jam’iyyun guda biyu da makiya mata, matasa da kuma sauran ‘yan Nijeriya.
Da yake gargadin magoya bayansa kan tashin hankali, ya ce jam’iyyarsa ba za ta taba barin wata kafa na yin magudi a zaben 2023.
“PDP da APC sun mutu, duk wanda ya san abin da yake yi kuma yana cikin hay-yacinsa ba zai sake shiga cikinsu ba ballantana har ma ya zabe su.
“Su ne tushen matsalolin da ke fuskantar ‘yan Nijeriya a halin yanzu kuma sun kasance makiyan matanmu da matasanmu da sauran ‘yan Nijeriya. Domin haka dole ne mu ki zabensu.
“Ya kamata ku kasance masu zaman lafiya kar ku fada cikin kowane tashin han-kali, amma ba za mu bari a sake maimaita zaben da ya gabata ba, domin haka duk mai jefa kuri’a ya kasance wakili wajen yin zabe da kuma tabbatar an kirga kuri’arsa,” in ji shi.